Hotuna: Wata mata ta tona asirin mijinta da yace mata ya tafi wajen kasuwanci ashe gidan wata matar aure ya tafi iskanci

Hotuna: Wata mata ta tona asirin mijinta da yace mata ya tafi wajen kasuwanci ashe gidan wata matar aure ya tafi iskanci

- Wata mata ta tonawa mijinta asiri, inda ta bayyana shirin da yake yi da wata matar aure domin suje su yi lalata a otel

- Matar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter, inda ta ce idan mijin matar ya gani yaje ya dauko matarsa a otel din da suke zaune

- Mijin dai ya yiwa matar tasa karyar cewa ya tafi kasar Afrika ta kudu ne domin yin kasuwanci

Wata mata wacce ta samu damar shiga shafin Twitter na mijinta ba tare da saninshi ba, ta sanya wata hira da yayi da wata matar aure a shafin nashi na Twitter, a lokacin da suke shirya yadda zasu hadu suyi lalata.

Hotuna: Wata mata ta tona asirin mijinta da yace mata ya tafi wajen kasuwanci ashe gidan wata matar aure ya tafi iskanci

Mijin ya tafi kasar Afrika ta Kudu domin gabatar da kasuwancinsa, amma kafin ya tafi, ya tuntubi matar auren a shafin Twitter, inda suka yi yarjejeniyar za su shafe kwanaki uku tare suna sheke ayarsu. Sai dai rashin sani yafi dare duhu, domin kuwa bai san cewa matarshi tana shiga shafinsa tana ganin abinda ke faruwa ba.

Hotuna: Wata mata ta tona asirin mijinta da yace mata ya tafi wajen kasuwanci ashe gidan wata matar aure ya tafi iskanci

KU KARANTA: Jaruman da suka fita daga masana'antar Kannywood sun fara dana sanin fita - Jarumi Shaba

Hotuna: Wata mata ta tona asirin mijinta da yace mata ya tafi wajen kasuwanci ashe gidan wata matar aure ya tafi iskanci

Matar ta rutsa su a shafin na Twitter inda ta bayyana cewa dole zata rabu da dan iskan mijin nata wanda bashi da aiki sai cin amanarta.

Da take wallafa hotunan irin hirar da yake yi da matar auren, tayi rubutu kamar haka: "Na shiga shafin Twitter na mijina bai kuma sani ba. Yanzu haka yana kasar Afrika ta kudu da matar wani mutumi a otel. Zaku iya taimaka mini ku nemo mijin matar nan yaje ya dauko matarshi, saboda ni na riga na yanke hukuncin rabuwa da wannan karen."

Hotuna: Wata mata ta tona asirin mijinta da yace mata ya tafi wajen kasuwanci ashe gidan wata matar aure ya tafi iskanci

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel