Bayan samun nasara a rumfar zabe, mun sake yin nasara a kotu Allah abin godiya, inji Sanata Abbo

Bayan samun nasara a rumfar zabe, mun sake yin nasara a kotu Allah abin godiya, inji Sanata Abbo

Kotun sauraron zaben majalisar dokokin tarayya dake zaune a Jihar Adamawa ya bayyana Sanata Elisha Cliff Abbo a matsayin wanda sahihin wanda lashe zaben dan majalisar dattawa mai wakiltar Adamawa ta Arewa a zaben da ya gabata.

Sanata Binta Masi Garba ta jam’iyyar APC ce wadda ta kalubalanci zaben na Abbo. Binta ita ce tsohuwar sanatar da ta wakilci yankin a majalisa ta 8.

KU KARANTA:Boko Haram: Gwamnan Yobe ya bayyana fushinsa a kan harin da aka kai maihaifarsa kwanan nan

Kotun zaben ta yanke wannan hukuncin ne a ranar Alhamis 29 ga watan Agusta, inda ta yi watsi da karofin da aka shigar a kan zaben Sanata Abbo daga bisani kuma ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben kamar yadda hukumar zabe ta INEC ta sanar a baya.

A wani dan takaitaccen bayani da ya wallafa a shafunkan sada zumunta dangane da wannan nasara, Abbo ya ce: “Ina taya al’ummar Madagali, Michika, Mubi ta arewa, Mubi ta kudu da Maiha murna. Munyi nasara a rumfar zabe ga shi kuma mun sake yin wata a kotu, Allah ne abin godiya.”

A ranar Litinin 29 ga watan Yuli, Sanata Abbo ya bada labarin yadda Rauf Aregbesola ya taba ba shi albashinsa na wata guda domin ya tsaya takarar shugabancin karamar hukumarsa a shekarar 2012.

Rauf Aregbesola, tsohon gwamnan Jihar Osun shi ne ministan tsaron cikin gidan Najeriya a yanzu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel