An bayyana wata Kabila guda daya a kasar nan da shugaba Buhari baya yiwa adalci

An bayyana wata Kabila guda daya a kasar nan da shugaba Buhari baya yiwa adalci

- An bayyana kabilar Nupe a matsayin kabilar da shugaban kasa Muhammadu Buhari baya yiwa adalci kwata-kwata a kasar nan

- Kabilar Nupe dai an bayyana cewa ita ce kabila ta biyar da tafi kowacce kabila yawan mutane a Najeriya

- Rahotanni sun nuna cewa tun hawan shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kujerar mulki bai bawa mutum ko daya daga wannan kabila mukami ba

Tun farkon mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ba a bai wa kabilar Nupe mukami ko guda daya ba, misalin minista ko shugaban wata babbar ma'aikata.

Kabilar Nupe dai sune kabila ta biyar da suka fi yawa a fadin Najeriya a yadda kidayar da aka gabatar a shekarar 1963 zuwa 1991 ta nuna.

Kabilar Nupe da suke da ilimi a bangaren boko da kuma kwarewa a fannin ayyukan Najeriya, sun bayar da gudumawa mai yawa a lokacin mulkin farko.

Da wannan dan karamin misalin dana bayar, ina so shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake tunani ya yiwa Nupawa adalci. Nupawa sun fito kwansu da kwarkwatansu sun zabi jam'iyyar APC saboda shugaba Buhari.

KU KARANTA: Dan Allah nan gaba indai za aje yiwa wani dan siyasar Najeriya duka a kirani zan bayar da gudummawa - Dan gidan Fela Kuti

Zan yi amfani damar domin jawo hankalin mutanen Neja da su daina nuna bangaranci idan har suna son su samu cigaba a jihar.

Jihar Neja wacce aka kirkirota a shekarar 1975 har yanzu tana daya daga cikin jihohin da suke samun koma baya, idan ka duba jihohin Jigawa, Katsina da basu wuce shekara ashirin da bakwai ba sunfi Neja samun cigaba.

Wannan rubutu dai duka wani mutumi ne ya rubuta mai suna Sulaiman Musa Wakili Bida, wanda yake zaune a jihar Kano a unguwar Mariri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel