Latest
Akalla mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) 63 ne suka sauya sheka zuwa APC mai mulki a karamar hukumar Idanre ta jihar Ondo a ranar Juma’ar nan.
An dade ana sauraron ruwan sama amma har yanzu babu. A dalilin haka Gwamna Bala Abdulqadir Mohammed ya tura wakilci wajen sallar rokon ruwa da aka shirya a jiya
An dauki bidiyon wani yanayi mai ban sha’awa na wata amarya da ke wasa da angonta inda suka ja hankalin mutane da dama. Ya nuna tsantsar shakuwa a tsakaninsu.
An samu labari cewa Alhaji Salihu Luman ya rubutawa PGF wasika, yana mai kira ga Gwamnonin APC a kan abubuwan da ke faruwa na ba Abdullahi Ganduje shugabanci.
Tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Legas, Alhaja Sinatu Ojikutu ta bayyana cewa fushin da Allah ke yi da 'yan Najeriya ne ya janyo aka shiga halin da ake ciki.
Sanata Victor Umeh mai wakiltar Anambra ta tsakiya, ya musanta raɗe-raɗin cewa sunayen ministocin shugaba Bola Tinubu sun dira majalisar dattawan Najeriya.
A halin da ake ciki, kowa ya kagu ya ji asalin mutanen da Bola Ahmad Tinubu zai nada a matsayin ministocinsa, sai dai har yanzu ba a san su waye ne ba tukuna.
Wasu ƙananan yara guda biyu sun riga mu gidan gaskiya a jihar Legas bayan katanga ta rufto akan gidansu a dalilin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi.
Majalisar dattawa ta bayyana cewa, za ta fasa zuwa hutu saboda ba zai yiwu ta tafi ba har sai an tantance ministocin Bola Ahmad Tinubu a wannan tsanin lokacin.
Masu zafi
Samu kari