Latest
Wata kotu a Kano ta dakatar da kamfanin KEDCO da hukumar NERC tilastawa kamfanoni biyan sabon kudin wutar lantarki har sai kotu ta kammala sauraron karar.
Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirinta na fara amfani da nukiliya wurin samar da wuta a kasar. Shugaban hukumar NAEC ne ya bada sanarwar a jiha Alhamis
Kwamishinan ruwa na jihar Gombe ya yi alkawarin magance matsalar ruwa a jihar zuwa ranar Asabar. Hakan na zuwa ne bayan rashin ruwa ya yi katutu a garin.
Bayan yada rahoton cewa wasu jami'an DSS guda biyu sun bindige matashi a gidan mai din Legas, hukumar ta ƙaryata cewa jami'anta ne suka aikata laifin.
Rundunar sojin Najeriya ta fara dibar sabbin sojoji masu kwalin sakandare domin inganta rundunar yayin da rashin tsaro ke kara kamari a fadin kasar baki daya.
Wasu hatsabiban 'yan bindiga sun sake kai mummunan hari a karamar hukumar Birnin Gwari a Kaduna inda suka sace Dagatai biyu da hallaka 'yan banga takwas.
Hukumar tsaron farar hula ta NSCDC ta tabbatar da cafke masu safarar man fetur daga jihar zuwa Katsina.Ta kama litar mai dubu ashirin, kuma ta mayar da su gidan mai.
Ministan Abuja ya nemi hadaka da kasar Hungary domin inganta noma da tsaro a birnin tarayya. Ya yi jawabin ne yayin wata ziyara da ya kai ofishin jakadancin kasar.
Daya daga manyan jam'iyyar PDP, Dele Momodu ya zargi Bola Tinubu da kokarin murkushe 'yan adawa.Ya ce PDP za ta dinke kafin zaben 2027 duk da kokarin Tinubu hana su.
Masu zafi
Samu kari