Latest
Wasu gungun ƴan daba sun kawo tashin hankali a kauswar Masallacin Idi a Kano bayan gwamnati ta ba ƴan kasuwa wa'adin sa'o'i 48 su tashi daga wurin gaɓa ɗaya.
Rundunar sojin saman Najeriya ta kai samame maɓoyar ƴan bindiga a yankin ƙaramar hukumar Bakori da ke jihar Katsina, an kashe ƴan ta'adda kimanin 29.
Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello bayan guje-guje da hukumar EFCC, zai gurfanar da kansa a gaban Babbar Kotun Tarayya a gobe Alhamis 13 ga watan Yuni a Abuja.
Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce nan ba da jimawa ba zai tura kudirin sabon albashin ma'aikata ga majalisar tarayya domin ta amince da shi.
Bayan Shugaba Bola Tinubu ya yi tuntube tare da zamewa a taro, mun kawo muku sauran shugabannin kasashe da suka hadu da irin wannan tsautsayi a duniya.
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya rubuta takarda ta musamman ga kwamishinan 'yan sanda a jihar domin samar da tsaro ga al'umma domin hawan salla.
Ranar 12 ga watan Yuni ta koma ranar dimokuradiyya a Najeriya shekarar 2018. Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya yi wannan sauyin a lokacin.
Tsohon mataimakin shugaban APC a Arewa maso Gabas, Salihu Lukman ya yi murabus a yau Laraba 12 ga watan Yuni inda ya ce babu shugabanci a jam'iyyar.
Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da shirin dawo da kai dalibai kasar Singapore domin cigaba da karatu. Gwamnan jihar, Umar A. Namadi ne ya sanar da haka.
Masu zafi
Samu kari