Sanusi II vs Aminu: Sarkin Kano Na 15 Ya Rubuta Takarda ga Ƴan Sanda Kan Hawan Sallah

Sanusi II vs Aminu: Sarkin Kano Na 15 Ya Rubuta Takarda ga Ƴan Sanda Kan Hawan Sallah

  • Yayin da ake ci gaba da rigimar sauratar Kano, da alama dai Sarki na 15, Aminu Ado Bayero zai yi hawa domin bukukuwan sallah
  • Aminu Ado ya rubuta takarda ta musamman ga jami'an 'yan sanda domin samar da tsaro ga al'ummar jihar Kano yayin bukukuwan
  • Wannan na zuwa ne yayin da Aminu Bayero ke shirye-shiryen hawa a babbar salla duk da kasancewar Sarki Muhammadu Sanusi II

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya rubuta takarda ta musamman ga kwamishinan ƴan sanda a jihar.

Aminu Ado Bayero ya rubuta takardar domin neman gudunmawar tsaro yayin bukukuwan sallah babba da za a yi a jihar.

Kara karanta wannan

Kallo ya koma sama: Sarkin Kano na 15 Aminu Bayero zai yi hawan babbar sallah

Aminu Ado ya tura takarda ga ƴan sanda a Kano kan hawan sallah
Aminu Ado Bayero ya roki ƴan sanda tsaro domin hawan sallah. Hoto: Masaraurar Kano.
Asali: Facebook

Kano: Aminu Ado ya godewa jami'an tsaro

Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda da sakatare na musamman ga Aminu Ado ya fitar a ranar 10 ga watan Yuni, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina rubuta wannan takarda a madadin Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero bayan umarnin kotu ta bukaci mayar da shi kan karaga."
"Ina amfani da wannan dama wurin isar da godiyarsa gare ku kan kokarin samar da tsaro da kuka yi musamman lokacin rigimar sarauta, jama'ar Kano suna godiya."

Aminu Ado ya roki jami'an tsaron hawan sallah

"Mai Martaba, ya roki shirya jami'an tsaro na musamman domin bukukuwa salla daga ranar Lahadi 16 ga watan Yuni zuwa Alhamis 20 ga watan Yuni, za a fara hawa daga fadar Nasarawa."
"Wannan hawa da bukukuwan sallah na da muhimmaci a bangaren addini da kuma aladu da ke jawo hankalin jama'a a ciki da wajen jihar Kano."

Kara karanta wannan

Kano: Bidiyon kwamandojin Hisbah a fadar Sarki Sanusi II, sun fadi matsaya

- Aminu Ado Bayero

Aminu Ado zai yi hawan Sallah

Kun ji cewa, yayin da ake ci gaba da dambarwa kan masarautar Kano, sarki na 15, Aminu Ado Bayero zai yi hawan babbar sallah kamar sallah yadda aka saba a al'ada.

Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi a ranar Talata.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rigimar saurautar jihar bayan tuge Aminu Ado Bayero a Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.