Kashim Shettima Ya Bayyana Yadda Tinubu Ya Gina Atiku da Sauran Mutane a Siyasa

Kashim Shettima Ya Bayyana Yadda Tinubu Ya Gina Atiku da Sauran Mutane a Siyasa

  • Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana Bola Tinubu a matsayin gwarzo a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya
  • Sanata Kashim Shettima ya fadi haka ne yayin da yake bayyana irin yadda shugaba Tinubu ya taimakawa yan siyasar Kudu da Arewa
  • Cikin waɗanda Kashim Shettima ya ambata har da Atiku Abubakar wanda shi ne babban abokin hamayyar shugaba Bola Tinubu a yanzu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima ya siffanta shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin gwarzon dimokuraɗiyya a Najeriya.

Sanata Kashim Shettima ya faɗi haka ne ganin yadda shugaban kasar ya dauki shekaru yana taimakon yan siyasa a kasar.

Kara karanta wannan

"Ina fatan lafiya": Atiku ya magantu bayan Tinubu ya zame har kasa a faifan bidiyo

Kashim Shettima
Kashim Shettima ya ce Bola Tinubu jigo ne a tarihin dimokuradiyyar Najeriya. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasar ya yi jawabin ne a lokacin wani taro da aka shirya domin murnar ranar dimokuraɗiyya a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima: "Tinubu mafaka ne ga 'yan adawa"

Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa ba za a taɓa mantawa da Bola Tinubu ba a tarihin jam'iyyun adawa a Najeriya.

Shettima ya ce a Bola Tinubu ya zama bango ne da dukkan ƴan adawa ke jingina da shi a lokacin mulkin PDP kuma ya yaki tsarin kafa jam'iyya daya a kasar.

'Yan siyasan da Bola Tinubu ya gina

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa Bola Tinubu ya gina yan siyasa da dama a dukkan bangarorin Najeriya, rahoton Daily Post.

Cikin manyan yan siyasa da Tinubu ya taimaka Shettima ya ambaci Atiku Abubakar, Olusegun Mimiko, Rauf Aregbesola da Adams Oshimole.

Kara karanta wannan

Tinubu ya faɗi ƙasa yayin taron ranar dimokuraɗiyya, fadar shugaban ƙasa ta yi martani

Tinubu ya ba Atiku Abubakar takara

Har ila yau Kashim Shettima ya ce a lokacin da aka kori Atiku Abubakar daga PDP wajen Bola Tinubu yaje neman mafita.

Ya ce a lokacin Bola Tinubu ya karbi Atiku Abubakar hannu biyu biyu har ma ya ba shi damar tsayawa takara a jam'iyyar AC.

Shettima ya fasa tafiya Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa Kashim Shettima ya fasa tafiyar da aka tsara zai wakilci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a taron kuwanci a Dallas.

Mataimakin shugaban ƙasar ya soke wannan tafiya ne sakamakon wata tangarɗa da jirginsa ya samu, ministan waje ne ya wakilci Tinubu a taron.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng