Latest
A jiya ne hukumar EFCC ta bukaci babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tuhumi manyan lauyoyin Najeriya guda biyu kan gaza gabatar da Yahaya Bello gaban kotu.
Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa akwai alamun za ta samu nasara a zaben gwamna da za a yi a jihar Edo a watan Satumba. Ahmadu Fintiri da Iliya Damagun ne suka fadi haka
'Yan bindiga sun kai farmaki garin Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja a jihar Katsina, sun yi awon gaba da mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara.
Shugaban kungiyar MURIC Farfesa Ishaq Lakin Akintola ya bukaci a soke dokar da ta ba gwamnatin jihar Sokoto damar sauke Sarkin Musulmi daga kujera.
Yan bindigan da suka yi garkuwa da limamin coci, Mikah Suleiman sun ɗauki bidiyonsa yana neman agajin mutane, ya ce rayuwarsa na cikin haɗari a wurin ƴan fashi.
Kungiyar gwamnonin Kudu, ta nemi gwamnatin Bola Tinubu da ta a yi la’akari da tsadar rayuwa da kuma yadda kowace jiha za ta iya biyan sabon albashi.
Hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta tattaro jabun kayayyaki daga Arewa maso Yamma na kasar nan da suka tasamma miliyoyin Naira.
Kamfanin man fetur na NNPC ya ƙaryata rahotannin da ke yawo a soshiyal midiya cewa ya zabtare farashin man fetur. Rahoton sabon farashin fetur "ƙanzon kurege ne."
Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta jaddada cewa babu rudani ko kadan dangane da rikicin masarautar Kano biyo bayan hukuncin babbar kotun tarayya
Masu zafi
Samu kari