Sadiya Haruna Ta Tona Asirin Aurenta da G Fresh, Ta Sha Mamaki a Daren Farko

Sadiya Haruna Ta Tona Asirin Aurenta da G Fresh, Ta Sha Mamaki a Daren Farko

  • Fitacciyar 'yar TikTok, Sadiya Haruna ta bude komai kan ainihin abin da ya haddasa rabuwarta da Al'ameen G-Fresh
  • Sadiya ta ce ta dauki G-Fresh a matsayin aboki ko kuma yaronta inda ta ce ko da kudi ba ta taba tsammanin aurensa ba
  • Sayyada ta ce amma daga bisani ta sha mamaki bayan shigowarsa dakinta a daren farko inda fahimci ba namiji ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Fitacciyar 'yar TikTok a Arewacin Najeriya, Sayyada Sadiya Haruna ta yi magana kan aurenta da Al'ameen G-Fresh.

Sadiya ta bayyana yadda suka faro soyayya da kuma abubuwa da dama da suka faru har suka rabu dutse a hannun riga.

Kara karanta wannan

"Munafurci ne": Jarumar fim ta caccaki Kiristoci kan murnan auren mawaki Davido

Sadiya Haruna ta magantu kan ainihin abin da ya raba da G-Fresh
Sayyada Sadiya Haruna ta yi martani kan ruguntsumin da ke cikin aurenta da G-Fresh. Hoto: @G Fresh alameen.
Asali: TikTok

G-Fresh: Sadiya Haruna ta caccaki mijinta

Matashiyar ta bayyana haka ne a bidiyon Youtube a hira da Hadiza Gabon a shirinta na Gabon's Room Talk Show.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sayyada ta ce tun farko Al'ameen G-Fresh yaronta ne ba ta taba tsammin za ta iya aurensa ba amma kaddara ya hada babu yadda aka iya.

Ta ce tun kafin auren sai suka yi rubutu kan cewa zai bar duk wasu halaye ciki har da bibiyan mata kuma ya amince har da rantsuwa.

Fitacciyar 'yar TikTok din ta ce komai na aurensu ita ta dauki nauyi hatta gidan da suke zaune ita ta kama haya har N1m.

"Ko da kudi ka ce zan auri G-Fresh ba zan yarda ba saboda abokina ne, kai yaro na ne ma saboda na sha zuwa Yahuza suya na bude gilashin mota ince gashi kasha ruwa."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Wata mata ta nemi taimakon ƴan Arewa, ta faɗi yadda wani mutumi ya cuce ta

"Daga baya ya fara soyayya da ni inda ban yi tsammanin da gaske yake ba, inda ya matsa daga bisani da naga ya shiga wani hali na amince amma da sharuda."

- Sadiya Haruna

"Na sha mamaki a daren farko" - Sadiya

Sadiya Haruna ta ce ta sha mamaki ranar da ya fara shigowa dakinta inda ta fahimci ba cikakken namiji ba ne inda har suka je neman taimako.

Kalli cikakken hirar a Youtube ko kuma ta shafin Facebook a nan:

Sadiya Haruna ta maka G-Fresh a kotu

Kun ji cewa tsohuwar jarumar Kannywood, Sadiya Haruna ta maka mijinta, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da G-Fresh, a gaban wata kotun shari'ar Musulunci.

Jarumar ta ce ta fahimci cewa mijin nata ba irin wanda take so ba ne, kuma ba za ta iya ƙarasa sauran rayuwarta tare da shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.