Latest
Rikici ya barke tsakanin masu nadin sarki a yankin Ofe da ke karamar hukumar Ose a Ondo inda suka koka kan yadda ake kokarin ƙaƙaba musu wani a matsayin sarki.
Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), ta ce a yanzu dai ta dakatar da batun shiga yakin aiki zuwa wani dan lokaci domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki.
Gwamnonin Najeeiya sun tabbatar da cewa ma'aikata za su amfana daga tattaunawar da ake yi kan sabon mafi ƙarancin albashi, sun ce za su ci gaba da tuntuɓa.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya ba da umarnin a cafko jami'an hukumar da suka kai samame ɗakunan otel a Legas.
Kamfanin jaridar This Nigeria ya zabi gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a matsayin gwarzon gwamna na shekarar 2024. An zabe shi ne saboda jarumta da ya nuna.
Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki (KEDCO) ta maka kungiyar masu sarrafa kayan abinci na kasa (MAN) gaban kotun babbar tarayya da ke Abuja saboda jawo asara.
Rikicin manoma da makiyaya a jihar Jigawa ya yi jawo asarar rayukan mutane uku a yankin gandun dajin Baranda da ke karamar hukumar Kiyawa, har an ceto wasu.
Wata babbar ma'aikaciyar gwamnati a jihar Abia ta shigar da wasu matasa su biyu kara babbar kotun jihar bisa zargin bata suna da suka mata. Ta nemi su biyata N100m
Rahotanni sun bayyana cewa kakakin majalisar jihar Edo ta kori wata 'yar majalisa daga zauren majalisar saboda ta yi shigar da ke nuna tsiraicinta.
Masu zafi
Samu kari