Latest
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya zargi wasu yan siyasa a Arewa da kokarin juya baya ga shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari kan manoma a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina. 'Yan bindigan sun hallaka mutum hudu har lahira a yayin harin.
Mutanen Abuja sun shiga zullumi lokacin da gidan tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okoracha ya ruguje. Gidan mai hawa biyar. Anceto mutane uku daga baraguzan.
Wani jami'i wanda ba a bayyana sunansa ba na hukumar yaki da masu yiwa tattaƙin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ya salwantar da ransa a birnin tarayya Abuja.
Babbar kotun jihar Osun ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga masu garkuwa da mutane da suka kashe wani Bafulatani bayan sun yi garkuwa da shi.
Kungiyar ma'aikatan jami'a ta kasa SSANU na shirin tsunduma yajin aiki a gobe Alhamis. Hakan ya biyo bayan wa'adin mako biyu da kungiyar ta ba gwamnati ne.
Alhaji Muhammad Abubakar Sa'ad III, sarkin Musulmi da ke Sokoto, ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin bin duk wata doka da gwamnatin jihar Sokoto za ta gindaya.
An samu asarar rayuka bayan aukuwar turmutsitsi a wurin wani taron addini a kasar Indiya. Da yawa daga cikin mutanen da suka rasa ransu mata ne da yara.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara gidan wani kwamandan 'yan banga da aka kashe domin yin ta'aziyya ga iyalansa. Gwamnan ya yi ruwan addu'a.
Masu zafi
Samu kari