Latest
Gwamnatin Tarayya ta gindaya sharuda kan adadin shekarun shiga manyan makarantu a Najeriya inda ta umarci hukumar JAMB ta tabbatar an bi wannan tsari.
Gwamnonin jam'iyyar PDP sun samu matsaya kan rikicin siyasar jihar Rivers tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Wike. Sun goyi bayan Fubara.
A jiya Laraba majalisar wakilai ta yi karatu na daya kan canza tsarin mulkin Najeriya da zai rika ba shugaban kasa da gwamnoni damar yin shekaru shida a kan karaga.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kwace wasu filaye da tsohuwar gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta yanka, sannan ta mayar wa makarantar da abin ta.
Daya daga cikin manyan makusantan siyasa na Peter Obi a Labour Party, Isaac Balami ya koma jam'iyyar APC wadda ya bari gabanin zaɓen shugaban kasa a 2023.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sake waiwayar mata yayin da yake ci gaba da rabon muƙamai, ya naɗa sabuwar shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana dalilin da ya sanya ake samun karuwar matsalar rashin tsaro a jihar. Gwamnan ya ce laifin ta'ammali da kwayoyi ne.
Masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP sun yi taro a Enugu inda suka koka kan halin da Najeriya ke ciki na wahala. PDP ta bukaci a zabe ta a 2027 domin saukaka rayuwa.
Uban jami'yyar NNPP, Dakta Boniface Aniebonam ya caccaki Sanata Rabiu Kwankwaso da hukumar INEC kan sauya tambari da kuma launin jam'iyyar gaba daya.
Masu zafi
Samu kari