Latest
Olusegun Obasanjo ya tona yadda cin hanci ya yi yawa a harkar matatun mai a Najeriya, ya fadi yadda masu kamfanin Shell suka koka kan rashawa a kan matatun.
'Yan Najeriya na ci gaba da tururuwa zuwa kan tituna domin nuna adawarsu kan halin kunci da tsadar rayuwar da aka samu a karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Babbar kotun jihar Legas ta tsawaita umarnin taƙaita wuraren da ya halatta masu zanga-zangar yunwa sun je a faɗin jihar domin tabbatar da zaman lafiya.
Daga karshe, Kungiyar ECOWAS ta yi magana kan zanga-zangar da ake yi a Najeriya inda ta jajantawa wadanda suka rasa rayukansu tare da ba da shawara.
Rundunar sanda a jihar Kano ta kama wani barawo da ya sace makudan kudi har N15m a karamar hukumar Kunci yayin da yake kokarin guduwa a jihar Katsina.
Gwamnatin Kano ta ce ta sassauta dokar hana fita ta awa 24 da ta sanya a fadin jihar. Gwamnatin jihar ya ce yanzu dokar za ta fara aiki 6 na safe zuwa 6 na yamma.
Masu shirya zanga-zangar da ake yi a jihar Legas sun sanar da tafiya hutun kwana ɗaya tal domin duba abubuwaɓ da suka faru da ɗaukarmataki na gaba.
Gwamnatin tarayya ta dauki matakin sanya masu daukar nauyin zanga-zanga cikin jerin wadanda ake nema ruwa ajallo. Za a yi caraf da su da sun shigo Najeriya.
Rundunar 'yan sandan Kano ta kama mutanen bisa zargin sata, lalata kadarorin jama'a da na gwamnati, tayar da hankula da gudanar da taro ba bisa ka'ida ba.
Masu zafi
Samu kari