Zanga Zanga: Kwamitin Zaman Lafiya, Gwamnati Sun Fara Tattaunawa da Tubabbun 'Yan Daba

Zanga Zanga: Kwamitin Zaman Lafiya, Gwamnati Sun Fara Tattaunawa da Tubabbun 'Yan Daba

  • Kwamitin zaman lafiya a Kano da hadin gwiwar ofishin mashawarcin gwamna na musamman a kan tsaro sun fara tattaunawa da matasa
  • Kwamitin da gwamnati sun fara ganawa da shugabannin tubabbun 'yan daba domin kawo karshen matsalar da ake fuskanta a jihar ta rashin tsaro
  • Bayan fara zanga-zanga a Kano, wasu 'yan daba daga sassan jihar sun far wa jama'a tare da kokarin jikkata jami'an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Kwamitin lafiya na jihar Kano da ofishin mashawarcin gwamnan Kano a kan harkokin tsaro sun fara tattaunawa da jagororin 'yan daba.

Kara karanta wannan

An kama matasa 632 a zanga zanga, kotu ta dauki matakin aika wasu zuwa kurkuku

Wannan ya biyo bayan tashe-tashen hankula a jihar bayan fara zanga-zangar kin manufofin Bola Ahmed Tinubu a ranar Alhamis.

kano map
Kwamitin zaman lafiya da gadin gwamnatin Kano na tattaunawa da matasa Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an shiga tattaunawar domin gano hanyar da za a magance mafa tsakanin jami'an tsaro da 'yan daba a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana kokarin shawo kan rashin tsaro

Shugaban kwamitin zaman lafiya na Kano, Ibrahim Waiya ya bayyana cewa duk da mazauna jihar na da hurumin kokawa a kan matsalar da kasa ke ciki, amma bai kamata a samu rashin tsaro ba.

A zantawarsa da Legit, Kwamred Ibrahim Waiya ya bayyana cewa sun fara ganawa da shugabannin 'yan daba 70 gabanin zanga-zangar.

Yadda ake wayar da kan jama'a

Kwamred Waiya ya ce su na shaidawa tubabbun 'yan daban muhimmancin wayar da kan matasan muhimmancin rayuwarsu domin masu tunzarasu sun killace 'ya'yansu.

Kara karanta wannan

Zargin kashe masu zanga zanga: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamitin bincikar jami'an tsaro

Ya kara da cewa matasa su na da muhimmanci, kuma wannan su ke son nunawa 'yan daban saboda su dauki rayuwarsu da muhimmancin gaske.

An mika masu jawo rashin tsaro kurkuku

A wani labarin, kun ji yadda kotun tafi da gidanka a Kano ta tesa keyar wasu matasa, daga cikinsu har da 'yan daba bisa zargin tayar da hatsaniya a sassan Kano.

Wannan na zuwa ne bayan jami'an tsaro sun cafke mutane akalla 632 da zargin tayar da hankula, fashe-fashen shaguna da wawashe kayan jama'a a lokacin gudanar da zanga-zanga a fadin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.