Latest
Kungiyar likitoci ta kasa NARD ta tafi yajin aiki saboda sace wata likita, Dr Ganiyat Papoola da yan bindiga suka yi a jihar Kaduna sama da wata bakawai da suka wuce
Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Ali Isa Ibrahim Pantami, ya yi magana kan hanyar kawo karshen 'yan bindiga da sauran matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
Mutum ɗaya ya rasa ransa a karshen makonnan a jihar Bayelsa lokacin da wani jirgin ruwa ya kife bayan ya ɗauko mutane a yankin karamar hukumar Ijaw ta Kudu.
Atiku Abubakar ya ce gwamnatin Tinubu ta dawo da tallafin man fetur a boye domin ta yi amfani da kudin wajen yakin neman zaben shekarar 2027 mai zuwa.
Gwamnan Gombe ya yi alkawrin karin albashin ma'aikata zuwa N70,000 bayan sun zauna da yan kwadago a jihar. Inuwa Yahaya ya ce suna daf da fara biyan sabon albashin.
A wannan labarin, za ku ji cewa kungiyar lauyoyi mata musulmi sun ce matsalar rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki ya fi shafar mata, an nemi daukin Tinubu.
Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya, Bennett Igweh, ya sha alwashin cafke ‘yan Shi'an da ke da alhakin kisan gillar da aka yi wa jami’ansa.
Kungiyoyin matasa za su maka gwamnan Sokoto a kotun ICC bisa zargin sakacin kisan sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa. Sun kafa sharuda ga gwamnan.
Jam'iyyar PDP reshen jihar Kogi ta fara shirin daukar matakin ladabtarwa kan sanata Dino Melaye biyo bayan sukar da ya yiwa shugabanninta na kasa.
Masu zafi
Samu kari