Latest
Awanni da kai samame ofishin kungiyar kare hakkin jama’a da tattalin arzikin kasa (SERAP) da ke Abuja, hukumar tsaro ta DSS ta bayyana cewa ba ta saba doka ba.
Kungiyoyin Arewa da Kudu sun bukaci Bola Tinubu ya rage kudin man fetur. Hausawa, Yarabawa da Ibo sun yi magana ga gwamnatin tarayya da murya daya.
Hadimin shugaban kasa a bangaren tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya fadi hanyar farfado da tattalin arziki inda ya ce dole sai an dakile fasa kwaurin mai zuwa ketare.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya amince da ba mutane izinin mallakar bindiga domin yakar yan ta'adda. Mutanen Arewa za su mallaki bindiga domin kare kansu.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya roki al'umma addu'o'i domin ubangiji ya hada kan attajiran jihar guda biyu, Aliko Dangote da Abdussamad Rabiu domin samun cigaba.
Hukumar DSS ta tsorata da barazanar kungiyar NLC inda ta sake shugabanta, Kwamred Joe Ajaero mintuna kafin wa'adin da aka gwamnatin Bola Tinubu ya cika.
Yayin da ya rage saura ƴan kwanaki kallilan, APC ta ɗage ranakun taron shugabanni da majalisar zartaswa NEC wanda sa ran yanke makamar Dr. Ganduje.
Kungiyar kwadago ta TUC ta bayyana cewa tana ganin ba cire tallafin mai ba ne asalin abin da ya kawo tsadar man fetur, ya ɗora laifin kan karya darajar Naira.
Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno ta ba ɗa umarnin a rufe makarantun sakandire da firamare saboda fargabar rasa rayuka a ambaliyar ruwa.
Masu zafi
Samu kari