Jam'iyyar APC Ta Canza Shawara kan Taron NEC da Za a Yanke Makomar Ganduje

Jam'iyyar APC Ta Canza Shawara kan Taron NEC da Za a Yanke Makomar Ganduje

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta ɗage tarukan da ta shirya gudanarwa a ranakun 11 da 12 ga watan Satumba, 2024 har sai baba-ta-gani
  • Sakataren watsa labaran APC na ƙasa ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar a daren ranar Litinin, 9 ga watan Satumba 2024
  • Morka ya sanar da cewa jam'iyyar APC za ta faɗi sababbin ranakun taron da zaran an zauna kuma an cimma matsaya nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki ta ɗaga taron shugabanni da majalisar zartaswa (NEC) har sai baba ta-gani.

Tun farko dai APC ta tsayar da ranakun 11 da 12 ga watan Satumba domin gudanar da tarukan biyu bayan amincewar shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Mazauna Kano sun tashi da takaici, an tsinci jaririya a ƙarkashin tayar mota

Shugaban APC Abdullahi Ganduje.
Jam'iyyar APC ta ɗage taruka biyu da ta shirya sai baba ta gani Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Sai dai sakataren yada labaran APC na kasa, Barista Felix Morka ya sanar da dage taron biyu a wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Litinin.

Jam'iyyar APC ta ɗage taron da ta shirya

A sanarwar da APC ta wallafa a shafinta na manhajar X, Feƙix Morka ya ce za a sanar da sabbbin ranakun tarukan nan gaba.

"Muna sanar da shugabanni da ƴan majalisar zartaswa na ƙasa NEC cewa an ɗage tarukan da aka shirya gudanarwa a ranakun 11 da 12 ga watan Satumba, 2024.

Ganduje zai san makomarsa a taron NEC

Ɗaya daga cikin abubuwan da ake tsammanin tattaunawa musamman a taron NEC shi ne batun kujerar shugabancin APC da Dr. Abdullahi Ganduje ke kai.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da sauran manyan ƙusoshin APC ne aka sa ran za su halarci taron idan an sake taaiɗa rana.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta dage ranakun komawa makaranta, ta fadi dalili

Legit Hausa ta fahimci cewa jam'iyyar APC ba ta bayyana ainihin dalilan da suka sa ta ɗauki matakin ɗage tarukan ba.

APC ta maida maratani ga Lukman

A wani rahoton kuma kalaman da tsohon mataimakin shugaban APC na ƙasa, Salihu Lukman, ya yi ba su yi wa jam'iyyar daɗi ba.

Jam'iyyar APC ta yi martani kan kalaman nasa inda ta bayyana cewa shi ma yana da alhaki a iƙirarin da ya yi na lalata Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262