Latest
Gwamna Abba Yusuf ya ce nan ba da jimawa ba za a fara biyan ma'aiktan jihar Kano sabon mafi karancin albashi na N70,000. Shugaban ma'aikatan jihar ya tabbatar.
Gwamnatin tarayya, ta bakin hukumar raya shiyyar Arewa maso Gabas ta bayyana cewa rashin kargon gini da cushewar ruwa a madatsar Alau ya jawo ambaliya a Maiduguri.
Gwamnatin Najeriya ta kashe N26m domin aikin gyaran madatsar Alau a ranar 29 ga watan Yulin 2024, kusan wata daya kafin ambaliyar ruwa ta mamaye Maiduguri.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hare-hare a jihar Zamfara da safiyar ranar Alhamis. 'Yan bindigan sun hallaka jami'an sojoji uku bayan sun bude musu wuta.
An shiga jimami a masana'antar shirya fina-finan Nollywood bayan sanar da rasuwar Shina Sanyaolu a jiya Laraba 11 ga watan Satumbar 2024 da muke ciki.
Shugabannin jam'iyyar APC na jihohin Najeriya da birnin Abuja sun yanke shawarar ganawa da Shugaba Bola Tinubu kan halin kunci da 'yan kasar ke fuskanta.
Matasan garin Moriki da Bello Turji ya ce zai kashe sun tsere cikin dare. Dan ta'addar ya ce zai kashe su ne idan ba a kawo masa kudi N30m daga garin Moriki ba.
A cikin labarin nan, gwamnatin Ebonyi ta kama wasu gidajen mai guda uku a babban birnin jihar, Abakaliki da yi wa jama'a algus, duk da tsadar da fetur ya yi.
Gwamnan jihar Jigawa, Ahmed Umar Namadi ya kaddamar da shirin rabon kayayyakin tallafi ga mutanen da bala'in ambaliyar ruwa ta ritsa da su a jihar.
Masu zafi
Samu kari