Latest
Shugaban kungiyar PAPSD kuma jagora a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Dakta Sani Shinkafi ya yabawa karamin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle.
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani da matar tsohon gwamnan jihar, Hadiza El-Rufai sun kaure a kafar sadarwa ta X kan gyaran rubutun Turanci.
Yusuf Kibiya ya samu goyon bayan mafi yawan jagororin jam'iyyar PDP a jihar Kano, inda ya samu nasara a kan abokan takararsa da suka hada da Nura Nuhu da Sani Aliyu.
Fitaccen mawaki Abdul D One ya shiga bakin jama'a bayan da ya saki bidiyon wakarsa mai taken 'Kibani Lokacinki'. Wakar ta samu karbuwa tare da jawo ce ce ku ce.
'Yan bindiga sun kai hari kan matafiya a jihar Zamfara. Daga cikin wadanda harin ya ritsa da su har da shugaban rundunar tsaro ta Askarawan Zamfara.
Makarantar Firamare ta Okugbe, Ikpide-irri, tana da malami daya tilo da ke koyar da dalibai sama da 170 wanda ya sa al'ummar yankin suka garzaya ofishin gwamnati.
Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta samu nasarar cafke wani matashi bisa zarginsa da cinnawa kakarsa wuta. Bincike ya nuna matashin na da tabin hankali.
Gwamnatin jihar Enugu ta tabbatar da kakaba biyan haraji a dakunan ajiye gawarwaki a kullum domin rage cinkoso musamman wadanda ba su dauke ta su ba.
Olumide Akpata, dan takarar Labour a zaben gwamnan Edo a 2024, ya bayyana matakin da ya dauka na kin kalubalantar sakamakon zaben da aka kammala kwanan nan a kotun.
Masu zafi
Samu kari