Latest
Tsohon shugaban Najeriya, Ibrahim Babangida zai kaddamar da littafin rayuwarsa a Abuja ranar 20 ga Fabrairu, 2025, tare da taron tara kudin gina gidan tarihi.
Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci sojoji su mamaye dazuka don murkushe 'yan bindiga, yayin da ya ziyarci Gwamna Bago don jajanta masa kan iftila'in Neja.
Gwamnan jihar Nasarawa, abdullahi Sule ya ziyarci kasar China domin tattaunawa da kamfanin batir na Lithium a Nasarawa. Za a rika ba ma'aikata albashin N500,000.
Hatsarin mota ya kashe matashiya mai shirin yiwa kasa hidima a hanyar Afikpo, Ebonyi. Sauran matasa sun ji rauni kuma an garzaya da su asibitin DUFUHS.
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ya yi jimamin mutuwar tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya, Janar Jeremiah Useni a rasu a yau Alhamis, 23 ga Janairu, 2025.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta bayyana irin barnar da gobara ta yi a kasuwar Karar Yan Katako da ke Sokoto. Ta ce shaguna da dama sun lalace.
Rahoto ya nuna cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane takwas a harin da suka kai jihar Benue tare da raunata wasu da dama.Yankin Tombo ya jima yana fama da rashin tsaro.
Gwamnatin jihar Kebbi ta ce ana ci gaba da daukar matakan da za su tabbatar da ingancin ilimi a jihar, daga cikinsu shi ne kara kudin ciyar da daliban makarantu.
Gwamnatin Tarayya ta ayyana kungiyar Lakurawa a matsayin ta ta'addanci tare da haramta ta da sauran kungiyoyin da ke da alaka da ita a Arewacin Najeriya.
Masu zafi
Samu kari