Kannywood: “Zan Biya Gaba Daya Bashin da Ake Bin Amunu S Bono” – Aisha Humaira

Kannywood: “Zan Biya Gaba Daya Bashin da Ake Bin Amunu S Bono” – Aisha Humaira

  • Fitacciyar jarumar Kannywood, Aisha Humaira ta nuna alhini kan babban rashi da masana'antar ta yi
  • A ranar Litinin ne Allah ya yi wa babban daraktan masana'antar shirya fina-finan Hausa, Aminu S Bono, rasuwa irin na farat daya
  • Jaruma Aisha ta dauki alkawarin biyawa marigayin gaba daya bashin da ake binsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Shahararriyar jarumar masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Aisha Ahmad Idris wacce aka fi sani da Aisha Humaira, ta nuna alhinin rashin babban darakta, Aminu S. Bono.

Marigayin ya yi mutuwar farat daya a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba, bayan ya bayyana cewar yana jin yar gajiya a tattare da shi.

Kara karanta wannan

Yan ta’adda sun bindige makanike har lahira, sun tafi da matarsa da yarsa a Nasarawa

Aisha Humaira ta ce za ta biya bashin da ake bin Aminu S Bono
Kannyood: “Zan Biya Gaba Daya Bashin da Ake Bin Amunu S Bono” – Aisha Humaira Hoto: Ayshatulhumairah/ aminusbono
Asali: Instagram

"Zan biyawa Aminu S Bono bashin da ake binsa", Aisha Humaira

Jaruma Aisha wacce ta bayyana marigayin a matsayin amininta kuma mai kaunarta a masana'antar, ta sha alwashin biya masa dukkan bashin da ake binsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata wallafa da ta yi a shafinta na Instagram jim kadan bayan sanar da labarin mutuwarsa, cikin hawaye an jiyo jarumar tana cewa:

"Tabbass Aminu S Bono mutumin kirki ne, na san shi tsawon lokaci, tunda na san shi ko musu bai taba hada ni da shi ba. Mutumina ne kwarai da gaske, amina ne mutum ne wanda yake matukar kaunata. Wanda dai duk wani abu da zai shafe ni ko na aiki ko na wani abu idan na ce Aminu kaza nake so, toh idan Allah ya so ya yarda zai yi iyakacin kokarinsa ya ga ya tsaya kan wannan abu har ya ga an cimma nasara.

Kara karanta wannan

Abdul Amart da Rarara sun yi wa iyalan marigayi Aminu S Bono sha tara ta arziki

"Ban san da wani irin abu zan iya saka masa kan wannan kauna da ya nuna mun a nan gidan duniya ba. Sakamakon haka ne ina kira ga dukkan wani wanda ya san cewar ya yi mu’amallar kudi da shi ko wani bashi ko ya karbi wani abun shi bai biya ba, In shaa Allahu Rabbi in dai har bai fi karfina ba na yi alkawari in shaa Allahu Rabbi zan sauke mashi nauyi. Idan so samuna ne kafin ma ayi jana’izarsa in sauke masa duk wani nauyi na bashi da yake kansa matukar bai fi karfina ba. Idan ya fi karfina kuma in shaa Allahu Rabbi zan yi kokari in nemo masa taimako a wajen wanda ya dace."

Har ila yau, ta ce idan har bashin da ake bin marigayin ya fi karfinta, za ta nema masa taimako a wajen da ya dace.

"Ina nemawa S Bono yafiyar jama'a", Jaruma Aisha

Kara karanta wannan

Ana tsaka da jin jiki a Najeriya, Sanata Yari ya ware 'yan Zamfara 1000 zai tallafa musu da magani

Ta kuma roki daukacin jama'a da Aminu ya yi wa laifi cikin sani ko bisa rashin sani da su taimaka su yafe masa, inta bayyana shi a matsayin mutumin kirki wanda ko musu bai taba shiga tsakaninsu ba.

Ga bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

dy_utrat85 ta yi martani:

"ALLAH ubangiji yajikanshi da rahama ALLAH ya kyauta namu zuwan. ALLAH yasaka miki da Alkhairi."

surykmata ta ce:

"Ubangijin mu Allahu ya saka maki da mafificin alkhairinSa @ayshatulhumairah ya sanya maki a mizani. Yadda ki ka gaggauta suturta Late Aminu Allah ya suturta ki duniya da lahira lokacin da kika fi komai bukatar sutura amn. Shi kuma Aminu Bono Allah ya karbi shahadar shi ya sa mutuwa hutu ce a gare shi. Allah ya duba bayan sa amn."

madam__korede:

"Innalillahi wainna ilaihi raj un Allah yagafarta masa ."

bilkisu__abdullahi:

"Allah ya biyaki ."

shehujuha_textiles:

"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Rajuun Wllh masoyin annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Sallam ne."

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da matarsa sun yi bikin cika shekaru 34 da aure

lauwalihonestygks

"Mutumin Kirki ne Allah Yajikansa da Rahama Yayafe Kura Kuransa Albarkachin Annabi Muhammad ﷺ "

Aminu S Bono ya rigamu gidan gaskiya

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa fitaccen darakta kuma jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa watau Kannywood, Aminu S Bono, ya riga mu gidan gaskiya.

Abokin aikinsa kuma shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Abba El-Mustapha, ne ya tabbatar da rasuwar Daraktan a shafinsa na Facebook ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel