Muna Goyon Bayan Soke Lasisin Yan Masana’antar Kannywood, Ali Nuhu

Muna Goyon Bayan Soke Lasisin Yan Masana’antar Kannywood, Ali Nuhu

  • Babban darakta kuma jarumin Kannywood, Ali Nuhu, ya yi mubaya'a ga matakin da gwamnatin Kano ta dauka na soke lasisin gaba daya yan masana'antar
  • Sarkin Kannywood ya ce suna goyon bayan shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar, Abba Al-Mustapha
  • Al-Mustapha ya ce sun dauki matakin ne don kawo gyara da tsaftace masana'antar ta shirya fina-finai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Shahararren jarumin masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu, wanda aka fi sani da Sarki ya goyi bayan soke lasisin yan masana'antar da gwamnatin jihar Kano ta yi.

Ali Nuhu ya jadadda cewar suna tare da shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar, Abba Al-Mustapha, dari bisa dari a kan wannan mataki da suka dauka na soke lasisin.

Ali Nuhu ya goyi bayan soke lasisin yan Kannywood
Muna Goyon Bayan Soke Lasisin Yan Masana’antar Kannywood, Ali Nuhu Hoto: Masoyan Ali Nuhu
Asali: Facebook

Ya kuma yi wa Al-Mustapha wanda ya kasance amininsa fatan sauke nauyin da Allah ya daura masa na shugabantar al'umma a masana'antar na shirya fina-finai.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Soke Lasisin Yan Kannywood Gaba Daya

Ali ya rubuta a shafinsa na Facebook:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Muna goyon bayanka, Allah ya bada ikon sauke nauyin Mai girma ES @abbaelmustapha1."

Dalilin soke lasisin

Da farko dai, mun kawo cewa gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ta soke gaba daya lasisin yan masa'antar ta Kannywood.

Da yake fayyace dalilin daukar wannan mataki, Almustapha ya ce hakan ya kasance ne saboda suna son tsaftace harkar fim gaba dayan ta domin a cewarsa ana abubuwa babu tsari a masana'antar ta fina-finai.

Martanin jama'a kan lamarin

Sani Ibrahim ya ce:

"Ai nasan bai isa ya fara wannan aikin ba tare da sahalewarku ba.
"Kunaso ku durkusar da Yara masu tasowa."

Najeeb Aminu Kura ya yi martani:

"Wannan shi ake kira haddin kai."

Abdulkarim Muhammad ya rubuta:

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Ali Nuhu Ya Taya Al'ummar Nijar Alhinin Halin Da Suke Ciki

"Muna godiya King da Kara karfin gwiwa #Favorite TANDARA."

Umar Babbah ya ce:

"Daman duk me kyakkyawan zuciya zai so abinda yazo dashi."

Usman Khaßir Muhd ya ce:

"Wannankuma Kai taragewa shidai zaiyi aikinsa bisa doka kurum."

Muhammad Maiguduma ya ce:

"A Gaskiya Muma da Nan Yan Jihar Adamawa Masu Kallon Finafinai Kannywood Munji Dadin Wannan Matsayin Da Aka Baiwa Abba El-Mustapha1 Allah Ya Tayasa Riko Ameen Summa Ameen ."

Mansur Saad Mari ya ce:

"Ameen
"Dole ku goyi baya gwamnati aiba ƙarya bace shima haka suka goyi bayanku shekera 8."

Ali Nuhu ya taya al'ummar Nijar alhinin juyin mulkin da sojoji suka yi

A wani labarin kuma, mun ji cewa Ali Nuhu ya yi tsokaci a kan halin da Jumhuriyar Nijar ke ciki sakamakon hambarar da gwamnatin farar hula da sojojin kasar suka yi.

Sarki Ali ya taya daukacin al'ummar kasar alhinin wannan yanayi da suka riski kansu a ciki na juyin mulki a wannan karni na 21.

Asali: Legit.ng

Online view pixel