Dillalan Fetur sun Zargi Kamfanin NNPCL da Hana su Mai

Dillalan Fetur sun Zargi Kamfanin NNPCL da Hana su Mai

  • Masu kasuwancin man fetur sun dora alhakin karancin man a kan kamfanin NNPCL, wanda su ka ce ba ya ba su man
  • Shugaban kungiyar PETROAN na kasa, Billy Gillis-Harry ne ya bayyana hakan yau Litinin yayin da kwastomomi ke ci gaba da kokawa
  • Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabo inda yan kasuwar bumburutu ke sayar da lita har akan ₦2000 a wasu wurare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos-Dillalan man fetur na kasa karkashin kungiyar Petroleum Products Retail Outlets Owners Association of Nigeria (PETROAN) sun dora alhakin matsalar man fetur a kan kamfanin NNPCL.

Ana ganin kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) shi ne babban mai shigo da man fetur din kasar kuma ya yi biris da ba su man.

Kara karanta wannan

Dillalan mai sun fadi lokacin da wahalar fetur da ta mamaye Najeriya za ta kare

Ana fuskantar matsalar man fetur a sassan Najeriya
Ana zargin kamfanin NNPCL da kin bawa yan kasuwar mai Hoto:Legit Hausa
Asali: Original

Shugaban kungiyar PETROAN na kasa, Billy Gillis-Harry ya shaidawa tashar Channels Television cewa NNPCL din ne ke da alhakin sayar mu su da man, kuma ba ya ba su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana ci gaba da layin man fetur

Masu ababen hawa sun shiga tsaka mai wuya bayan karancin man fetur a gidajen man, inda masu ababen hawa su ka kafa layi.

Jihohin da ake samun layin mai masu tsayi sun hada da Abuja, Kano, Kaduna, Gombe, Sakkwato da kuma Benuwai.

Baya ga karancin man, ana fuskantar tsadar fetur a gidajen mai da dama inda ake sayar da lita a kan N700 zuwa N1200.

Masu kasuwar bayan fage da ake kira yan bumburutu yanzu haka na cin karensu babu babbaka, domin wasu na sayar da litar man har Naira 2000.

Karancin man yana ci gaba da jefa yan Najeriya cikin kunci rashin walwala, kamar yadda Nairaland ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wahalar man fetur ta jawo tashin farashin motoci da sauran abubuwan hawa

Kudin mota ya karu saboda fetur

Ana da labari karancin man fetur a sassan Najeriya ya janyo karuwar kudin mota a jiho daban-daban har da babban birnin tarayya Abuja, Kano da jihar Kwara.

A birnin Ilorin, mazauna yankin sun koka kan yadda farashin ke ninkawa tun bayan bullar karancin mai, inda aka biyan Naira 200 a wuraren da a da ake biyan Naira 100 a da.

Asali: Legit.ng

Online view pixel