Kano: Dilan Wiwi Da ’Yan Sanda Ke Nema Ruwa a Jallo Ya Shiga Hannu

Kano: Dilan Wiwi Da ’Yan Sanda Ke Nema Ruwa a Jallo Ya Shiga Hannu

  • A kokarinta na tabbatar da yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama dilan wiwi, Badoo
  • Tsawon lokaci rundunar ta dauka tana neman Badoo, wanda asalin sunansa Sadam Mu’azu kan zargin safarar miyagun kwayoyi
  • Daga cikin kayayyakin da aka kwato a yayin kama mai laifin akwai fakiti 11 a tabar wiwi, babura biyar da tsabar kudi N111,500

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wani kasurgumin dillalin miyagun kwayoyi da aka fi sani da ‘Badoo’ da wasu mutane takwas da ke da hannu a ciki.

'Yan sandan Kano sun kama rikakken dilan miyagun kwayoyi
Kano: 'Yan sanda sun kama Badoo, dilan miyagun kwayoyi da ake bena ruwa a jallo. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Rundunar 'yan sanda ta jima tana neman Sadam Mu’azu mai shekaru 33 a unguwar Tukuntawa a Kano, ruwa a jallo kan safarar miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

Dillalan mai sun fadi lokacin da wahalar fetur da ta mamaye Najeriya za ta kare

Yadda 'yan sanda suka kama Badoo

Mazauna yankin sun sha kai rahoton Saddam ‘Badoo’, a matsayin babban dilan miyagun kwayoyi, ciki har da tabar wiwi, kuma yana rabawa matasa da matan aure a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a shafinsa na Facebook, ta tabbatar da nasarar kama Badoo.

Kiyawa ce kama Badoo ya biyo bayan jajircewar tawagogin sashen yaki da daba karkashin SP Hussaini Gimba, da na ofishin ‘yan sanda na Sharada, karkashin CSP Bilyaminu Bello.

Abubuwan da aka kwato a hannun Badoo

Tagawagogin sun gudanar da aikin sa ido tare da tattara bayanai wanda hakan ya kai ga kama Badoo da abokan harkallarsa a ranar 22 ga Afrilu, 2024, jaridar Leadership ta ruwaito.

A yayin kai samamen, 'yan sanda sun gano wasu tarin hujjoji da suka shafi laifukan da ake tuhumar masu laifin ciki har da fakiti 11 da ake zargin tabar wiwi ce da kuma adda.

Kara karanta wannan

Ondo: An kashe kodinetan yaƙin neman zaben gwamnan APC, 'yan sanda sun magantu

Sauran sun hada da babura guda biyar da ake kyautata zaton ana amfani da su wajen rarraba kwayoyin ne da kuma tsabar kudi sama da Naira 111,500.

Kotu ta dage shari'ar Ganduje

A wani labarin kuma, babbar kotun jihar Kano, ta dage shari'ar tuhumar rashawa da aka shigar kan tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, iyalansa da wasu makusantansa.

Kotun za ta fadi matsayarta kan yiwuwar ba da izinin a mikawa wadanda ake tuhuma takardar sammaci ba gaba da gaba ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel