Akwai Kura: Isra'ila Ta Sake Yi Wa Iran Lahani, Ta Hallaka Babban Minista

Akwai Kura: Isra'ila Ta Sake Yi Wa Iran Lahani, Ta Hallaka Babban Minista

  • Rundunar sojojin Isra'ila na ci gaba da kai hari kan manyan jami'an gwamnatin jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • A cikin 'yan kwanakin nan Isra'ila ta kashe shugaban majalisar tsaron Iran, Ali Larijani da babban kwamandan dakarun Basij
  • A ranar Laraba, 18 ga watan Maris 2026, rundunar sojojin Isra'ila ta sanar da cewa ta kashe Ministan leken asiri na Iran a wani hari da ta kai

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Rundunar sojojin Isra'ila ta sanar da hallaka Ministan leken asiri na Iran, Esmaeil Khatib.

Rundunar IDF ta bayyana cewa ta hallaka Ministan leken asirin ne a wani hari da aka tsara aka kai masa a Tehran.

Isra'ila ta kashe Ministan leken asiri na Iran
Sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei
Source: Getty Images

Rundunar IDF ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta sanya a shafinta na X a ranar Laraba, 18 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Bayan kashe manyan jagorori 2 a Iran, Isra'ila ta fadi shirinta kan Mojtaba Khamenei

A cewar sanarwar Khatib ya taka muhimmiyar rawa lokacin zanga-zangar baya-bayan nan a duk faɗin Iran, ciki har da kamawa da kisan masu zanga-zanga.

Rundunar ta ce ya jagoranci ayyukan ta'addanci ga Isra'ilawa da Amurkawa a duniya baki ɗaya. Haka kuma, ya gudanar da ayyuka kan 'yan ƙasar Iran lokacin zanga-zangar Mahsa Amini (2022–2023).

A cewar rundunar ma'aikatar leken asiri ta Iran tana da manyan kwararan dabarun leken asiri, tana kula da sa ido, leƙen asiri, da kuma gudanar da ayyukan sirri a duniya baki ɗaya, musamman kan 'yan ƙasar Isra'ila da na Iran.

Wannan kisan ya zo ne yayin da yaƙin da Amurka da Isra'ila ke jagoranta a kan Iran ya shiga rana ta 19, inda Isra'ila ta tsananta ayyukanta na soja a duk faɗin yankin.

Tashar Aljazeera ta ce wakilinta a West Bank Nida Ibrahim ya ce masu fashin baki kan harkokin sojoji na Isra'ila suna kallon Esmaeil Khatib a matsayin amintaccen jigo na kusa da sabon jagoran ƙoli na Iran, Mojtaba Khamenei.

"A cewar majiyoyin Isra'ila, sun ce sun kasance suna tattara bayanan sirri da suka ba su damar ayyana mutuwar manyan jami'an Iran guda uku a cikin sa'o'i 24 da suka gabata."

Kara karanta wannan

Rudani: Shugaban majalisar tsaron Iran ya fitar da sanarwa bayan Isra'ila ta ce ta kashe shi

- Nida Ibrahim

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya tabbatar da cewa Isra'ila ta kashe Esmaeil Khatib, a wani hari da aka kai a daren jiya.

Kisan na sa ya zama kisan gilla na uku da aka yi wa babban jami'in gwamnatin Iran a cikin kwanaki biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng