Sarki Salman Ya Kira Shugaba Buhari Ta Wayar Salula, Ya Masa Ta'aziyyar Mutuwar Janar Attahiru

Sarki Salman Ya Kira Shugaba Buhari Ta Wayar Salula, Ya Masa Ta'aziyyar Mutuwar Janar Attahiru

- Sarki Salman na ƙasar Saudiya yayi wa shugaban ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ta'aziyyar mutuwar shugaban sojin ƙasa, Janar Attahiru, ta wayar salula

- Mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu, shine ya bayyana haka a shafinsa na dandalin sada zumunta

- Hakanan kuma, shugaba Buhari da Sarki Salman sun taya juna murnar kammala azumin watan Ramadana

Sarki Salman Ibn Abdul'azeez na ƙasar Saudi Rabia ya kira shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a waya domin yi masa ta'aziyyar rasuwar shugaban rundunar sojin ƙasa, Janar Ibrahin Attahiru tare da wasu jami'ai 10 a hatsarin jirgi.

KARANTA ANAN: FG Ta Ɗauki Nauyin Ɗaliban Kwalejin FCFM Kaduna da Aka Sace, Zata Canza Musu Wurin Zama Na Wucin Gadi

Sarkin yayi jimamin wannan babban rashi da Najeriya tayi tare da miƙa ta'aziyyar sa ga shugaba Buhari a yayin da suka zanta a wayar salula ranar Litinin.

Sarki Salman Ya Kira Shugaba Buhari Ta Wayar Salula, Ya Masa Ta'aziyyar Mutuwar Janar Attahiru
Sarki Salman Ya Kira Shugaba Buhari Ta Wayar Salula, Ya Masa Ta'aziyyar Mutuwar Janar Attahiru Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, shine ya bayyana haka a shafin sa na dandalin sad zumunta tuwita @GarShehu.

KARANTA ANAN: Bayan Ƙin Halartar Jana’izar COAS, Shugaba Buhari Yayi Magana da Matar Janar Attahiru a Waya

Garba Shehu yace:

"A yau Litinin, shugaban ƙasa Buhari ya zanta da sarki Salman Ibn Abdul'azeez na ƙasar Saudiyya, lokacin da ya kira shi ya masa ta'aziyyar rasuwar shugaban sojin ƙasa, Ibrahim Attahiru, tare da wasu jami'ai 10."

"Sarkin ya taya yan Najeriya baki ɗaya jimamin wannan babban rashi na manyan sojojin da suke alfahari da su."

Hakanan kuma, shugaba Buhari da Sarki Salman sun taya juna murnar sallar Idi (Eidul Fitr) bayan kammala wata ɗaya cur ana azumin Ramadana.

A wani labarin kuma Wani Mutumi Yayi Yunƙurin Hallaka Limamim Ka'aba a Makkah

Rahotanni daga ƙasar Saudiyya na nuni da cewa wani mutumi yayi yunƙurin kashe limamin ka'aba ranar Jumu'a.

Hukumar dake kula da masallatai biyu masu daraja a ƙasar ce ta bayyana haka a shafinta na kafar sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel