An Kama Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump Gabannin Gurfanar Da Shi

An Kama Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump Gabannin Gurfanar Da Shi

  • Tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, na tsare a hannun yan sanda gabannin gurfanar da shi
  • Ana sa ran Trump zai dangwala zanen yatsunsa duk a shirye-shiryen gurfanar da shi, amma babu tabbacin ko za a dauki hoton fuskarsa
  • An tattaro cewa tsohon shugaban Amurkan zai fuskanci tuhume-tuhume 30 da suka hada da zamba

Amurka - An kama tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump a hukumance kuma a yanzu haka yana tsare a hannun yan sanda gabannin gurfanar da shi bayan ya isa wata kotu a unguwar Lower Manhattan.

A cewar CNN, za a dauki hoton zanen yatsun tsohon shugaban kasar amma ba a tabbatar da ko za a dauki hoton fuskarsa ba.

Tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump
An Kama Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump Gabannin Gurfanar Da Shi Hoto: Donald Trump
Asali: Getty Images

Dalilin da yasa aka kama Donal Trump

Biyo bayan haka, za a gabatar da Trump a kotu don gurfanar da shi a gaban kuliya, lamarin da ake sa ran zai kasance cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Lafiyarsa lau: Bayan dogon cece-kuce, hoton Tinubu da matarsa ya bayyana a kasar waje

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan kamun nasa, ba a sa ran yan sanda za su sanya masa ankwa saboda zai ci gaba da kasancewa karkashin kulawar tsaro.

A hukumance, Trump ne shugaban kasar Amurka na farko da zai fuskanci tuhuma bisa zargin aikata laifi yayin da ya gurfana a kotu bayan an tuhume shi.

Sashin Hausa na BBC ya rahoto cewa ana zargin tsohon shugaban kasar da biyan wata mai fina-finan batsa, Stormy Daniels toshiyar baki don kada ta yi bayani game da alakar nema da ke tsakaninsu a lokacin da yake neman takarar shugabancin kasa a 2016.

CNN ya rahoto a baya cewa tsohon shugaban kasar zai fuskanci tuhume-tuhume 30 da suka hada da zamba don dakatar da biyan kudaden da aka yi wa wata jarumar wasan batsa a 2016.

Ba za a kafa gwamnatin wucin gadi ba a Najeriya, Fitaccen fasto

Kara karanta wannan

Rikicin siyasa: 'Yan APC da PDP sun kaure da kazamar fada a wata jiha, an harbi wani

A wani labari na daban, shahararren faston nan na Najeriya kuma shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele ya ce babu abun da zai hana rantsar da sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu.

Primate Ayodele na martani ne ga rade-radin da ake yi na cewa wasu yan siyasa a kasar suna kulla-kulla don kafa gwamnatin wucin gadi tare da hana rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel