Da Duminsa: An Saka Ranar Bikin Nadin Sarautar Sarki Charles na III

Da Duminsa: An Saka Ranar Bikin Nadin Sarautar Sarki Charles na III

  • Fadar Buckingham ta sanar da cewa za a yi shagalin bikin nadin sarautar Sarki Charles III a ranar 6 ga watan Mayun 2023
  • Kamar yadda fadar ta bayyana, Archbishop na Canterbury ne zai yi jagoranci a Westminster Abbey dake Landan
  • Har ila yau, an bayyana cewa a wannan shagalin bikin ne za a nada matar Sarkin Camilla ta kasance sarauniya

Za a yi shagalin bikin nadin sarautar Sarki Charles III a ranar Asabar 6 ga watan Mayun 2023.

Za a yi shagalin ne a Westminster Abbey, kamar yadda fadar Buckingham ta sanar.

Sarki Charles III
Da Duminsa: An Saka Ranar Bikin Nadin Sarautar Sarki Charles na III. Hoto daga punching.com
Asali: UGC

Jaridar Punch ta rahoto cewa, a ranar za a yi nadin Sarauniya Camilla.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Hotuna da Bidiyon Sojan Dake Satar Makamai Yana Kaiwa ‘Yan Bindiga Yayin da Dubunsa ta Cika

Takardar da iyalan gidan sarautar suka fitar mai taken,

“Nadin sarautar Mai Martaba Sarki.”

Takardar tace:

“Fadar Buckingham na farin cikin sanar da cewa za a yi nadin sarautar Mai Martaba Sarki a ranar 6 ga watan Mayun 2023.
“Za a yi nadin sarautar a Westminster Abbey dake Landan kuma Archbishop na Canterbury ne zai jagoranci.
“A shagalin za a ga yadda za a nada Mai Martaba Sarki Charles III tare da Sarauniyarsa.
“Nadin sarautar zai duba rawar da basaraken ya taka a yau kuma zai duba na gaba yayin da ake kafa tsohon tarihi.
“Za a sanar da karin bayani nan gaba.”

Jerin Kadarorin da Sarauniya Elizabeth II Ta Bar wa Yarima Charles da Kimarsu

A wani labari na daban,sarauniya Elizabeth II ta rasu a jiya Alhamis 8 ga watan Satumban 2022. Ta shekara 96 kafin Allah ya karbi ranta a gidanta dake Scotland.

Ta bar tarin dukiya mai yawa da aka ce ta kai sama da dala miliyan 500, wanda kuma danta Yarima Charles ne zai gada ya ci gaba da cin duniyarsa da tsinke.

A cewar wani rahoto na Fortunes, mafi yawan kadarorin sarauniyar mallaki ne na Royal Firm, ciki har da dala biliyan 28 na gidan sarautar Burtaniya da Sarki George VI da Yarima Philip suka ambata a matsayin kasuwancin ahali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel