Hotuna da Bidiyon Sojan Dake Satar Makamai Yana Kaiwa ‘Yan Bindiga Yayin da Dubunsa ta Cika

Hotuna da Bidiyon Sojan Dake Satar Makamai Yana Kaiwa ‘Yan Bindiga Yayin da Dubunsa ta Cika

  • Dakarun sojin Najeriya sun yi ram da wani Soja mai suna Iorliam Emmanuel kan zarginsa da satar makamai rundunar
  • ‘Dan asalin jihar Binuwai din yana kai wa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne makaman da yake sata kamar yadda Zagazola Makama ya bayyana
  • Yana aiki da 156 Task Force Bataliya dake garin Mainok a jihar Borno a karkashin rundunar Operation Hadin Kai

Borno - Rundunar sojin Najeriya ta damke wani soja da ake zargi da satar makamai tare da kaiwa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne.

Kamar yadda kwararre a kiyasin tsaro, Zagazola Makama ya bayyana a shafinsa na Twitter, yace sojan mai suna Iorliam Emmanuel dubunsa ta cika.

‘Dan asalin jihar Binuwai din yana aiki ne da 156 Task Force Battalion dake Mainok a jihar Borno a karkashin rundunar Operation Hadin Kai.

Kara karanta wannan

'Dan wasan kasar Amurka Zai Fita daga Duniya Domin Ya Shirya Wani Sabon Fim

Sojan Najeriya
Hotuna da Bidiyon Sojan Dake Satar Makamai Yana Kaiwa ‘Yan Bindiga Yayin da Dubunsa ta Cika. Hoto daga @ZagazOlamakama
Asali: Twitter

A bidiyon da Zagazola Makama ya fitar, an ga sojoji suna cire makamai daga jikin wanda ake zargin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ka ga rayuwarka ko? Zaka je ka kai wa Boko Haram wadannan abubuwan yadda zasu zo su kawo mana hari a wannan sansanin. Kada ka damu, Allah ya fi ka.”

- Aka ji wani yana fadi a bidiyon da harshen turanci.

“Duk wadannan ma sun tsufa, sun to tsatsa.”

- Aka ji wani soja yana fadi inda yake nufin harsasan da ke jikin wanda ake zargin.

Nasara daga Allah: NAF Sun Sheke Rikakken Shugaban ‘Yan Bindiga, Ali Dogo

A wani labari na daban, dubu Shugaba kuma gagararren ‘dan ta’addan jihar Kaduna, Ali Dogo, ta cika inda sojoji suka aika shi lahira tare da wasu mayakansa sakamakon luguden wuta ta jiragen yaki da aka yi musu a karamar hukumar Giwa ta jihar.

Kara karanta wannan

Abinda Ya Kamata Ka Sani Game Da Malaman Musulunci 5 da Buhari Zai Ba Lambar Karramarwa Yau

An gano cewa dakarun rundunar Operation WHIRL Punch ne suka a kwanakin karshen mako da ya gabata.

Wata majiyar tsaro ta sanarwa PRNigeria cewa Dogo da mabiyansa sun tsero daga jihar Niger zuwa karamar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna sakamakon luguden wutan da aka matsanta musu a maboyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel