Najeriya Ta Shiga Sahun 5 na Farko na Kasashen da Bankin Duniya ke bi bashi

Najeriya Ta Shiga Sahun 5 na Farko na Kasashen da Bankin Duniya ke bi bashi

  • Sabon rahoton bankin Duniya ya nuna kowace kasa ta na rage bashin da ke wuyanta a yau
  • Amma Najeriya ta na kara tunkarar matsi ne domin kudin da bankin Duniya ke binta ya karu
  • Babban bankin Duniyan yana bin Gwamnatin Najeriya bashin fiye da Naira tiriliyan 5 a 2022

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Yawan karbo aron kudi da gwamnatin tarayya take yi, ya jawo Najeriya ta shiga cikin kasashen da ke da tulin bashin kasar waje a kan su.

Rahoton Punch na ranar Talata, 9 ga watan Agusta 2022, ya nuna Najeriya ta motsa a jerin sahun 'yan farko na kasashen da ake bi bashin kudi a Duniya.

Rahoton da bankin Duniya ya fitar na kashe-kashen kudi a 2021, ya nuna Najeriya ce kasa ta biyar a wadanda suka ci bashin bankin da ke Amurka.

Kara karanta wannan

Ministoci Sun Samu Sabani a Taron FEC, Shugaban Kasa ya Raba Masu Gardama

A shekarar 2021, bankin yana bin gwamnatin Najeriya bashin Dala biliyan 11.7, kusan Naira Tiriliyan biyar a kudin gida. Yanzu har bashin ya fi haka.

An karbo aron $1.3bn a 2022

Kamar yadda jaridar ta kawo labari dazu, zuwa karshen watan Yuni, abin da ake bin Najeriya bashi ya kai Dala biliyan watau fiye da N5.4tr kenan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sabon rahoton da aka fitar ya tabbatar da cewa a cikin shekara daya, Najeriya ta karbo aron $1.3bn.

Bankin Duniya
Bankin Duniya Hoto: www.worldbank.org

Wannan karin bashi ya jawo Najeriya ta motsa a jeringiyar kasashe masu bashi a kansu. Da wannan kari kasar ta zama ta hudu, da yiwuwar kara gaba.

Kasashe sun rage abin da ake binsu

Yawon karbo aron da gwamnatin Muhammadu Buhari take yi, ya yi sanadiyyar da aka sha gaban kasar Vietnam wanda ake bi bashin fam $14bn a bara.

Kara karanta wannan

2023: Ku kwantar da hankali, za a yi zaben 2023 ba tare da wata matsala ba, hafsan tsaro

A kasashen da ke da yawan bashi a kansu, kowa ya rage nauyin da ke 2022 illa Najeriya. Indiya da ke ta farko ta iya rage bashin ta da $2.3bn a bana.

Ga jerin kasashe n da abin da bankin ke binsu:

1. Indiya Dala Biliyan 19.7

2. Bangladesh Dala biliyan 18

3. Fakistan Dala biliyan 15.8

4. Najeriya Dala biliyan 13

5. Vietnam Dala biliyan 12.9

Jaridar The Eagle tace duk wannan bashi dabam yake da wasu $486 da gwamnatin Najeriya ta karbo aro domin yin gine gine da kawo ayyuka na cigaba.

Bashin Paris Club

Rahoto ya zo cewa Shugaban Najeriya ya hana a fara cire bashin da ake bin Gwamnonin Jihohi daga tsohuwar yarjejeniyar Paris Club.

Ministar kudi da Ministan shari'a sun roki a soma karbe bashin daga FAAC, amma majalisar FEC ta rinjaya a kan ra’ayin Gwamnonin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel