Rashin tsaro: Shugaban Rasha, Putin ya yi wa Gwamnatin Buhari muhimmin alkawari

Rashin tsaro: Shugaban Rasha, Putin ya yi wa Gwamnatin Buhari muhimmin alkawari

  • Vladimir Putin ya ba Najeriya tabbacin gwamnatin kasar Rasha za ta ba ta gudumuwa
  • Shugaban na Rasha yace za su taimakawa gwamnatin Najeriya wajen yaki da ‘yan ta’adda
  • Putin ya bayyana haka ne da Jakadan Najeriya, Farfesa Abdullahi Shehu ya kai masa ziyara

Russia - Yayin da ake kokarin kawo karshen Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda a Najeriya, shugaba Vladimir Putin ya yi alkawarin taimakawa Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin yace zai yi bakin kokarinsa wajen maganin duk wasu ‘yan ta’adda a kasar nan.

Vladimir Putin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Jakadan Najeriya zuwa Rasha, Farfesa Abdullahi Shehu wanda ya gabatar da takarda gare shi.

Da yake bayani a fadar gwamnati ta Kremlin, Putin yace gwamnatinsa za ta yi duk abin da za ta iya domin kauda masu tsattsauran ra’ayin addini a duk Duniya.

Kara karanta wannan

EFCC ta cigaba da gabatar da hujjoji a kotu da za su sa a daure tsohon gwamna Fayose

Alakar Najeriya da Rasha

Putin ya yi magana kan dangantakar da ke tsakanin Najeriya da kasar Rasha, yace za su tattauna a kan yadda za a magance ta’addanci da sauran wasu matsaloli.

The Guardian ta kawo rahoto a ranar 2 ga watan Disamba, 2021, inda aka ji Putin ya na cewa Rasha a shirya take ta amfana da kasashe, kuma a amfana da ita

Shugaban Najeriya
Buhari a taron UN Hoto: @FemiAdesina
Asali: Facebook

Shugaban yace za a cin ma wannan idan akwai ganin girma da mutunta juna, tare da jan-kunne ga kasashe su guji yi wa junansu katsalandan cikin harkokinsu.

Kawo karshen COVID-19

Har ila yau, an rahoto Putin yana fadawa Farfesa Shehu cewa Rasha ta kirkiro maganin cutar COVID-19, kuma ta shirya raba shi ga sauran kasashen Duniya.

Ganin yadda cutar COVID-19 ta addabi kasashe a yau, Putin yace sun kirkiro maganin wannan cuta, kuma duk kasar da take da sha’awa, sai tayi mata magana.

Kara karanta wannan

Bayan Twitter, gwamnatin Buhari za ta sanya wasu ka'idoji kan NETFLIX da sauransu

Jakadan Najeriya a Rasha ya ji dadin wannan tattaunawa da ya yi da Vladimir Putin, har ya kara masa da cewa takwaransa, Muhammadu Buhari ya na gaida shi.

Kul aka raba Najeriya - Osinbajo

Yemi Osinbajo ya ce Muhammadu Buhari na bakin kokarinsa, ya kuma yi alkawari: Gwamnatin APC za ta kawo karshen matsalar rashin tsaro kwanan nan.

Farfesa Yemi Osinbajo ya kuma ja-kunnen mutane da cewa neman a raba kasar nan ba zai haifar da ‘da mai ido ba, sai karin wahala da za ta nunku a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel