Sudan: Tsauraran matakai 3 da sojoji su ka ɗauka bayan kama Firayim Minista Hamdok

Sudan: Tsauraran matakai 3 da sojoji su ka ɗauka bayan kama Firayim Minista Hamdok

  • Guguwar juyin mulki ta fada kasar Sudan, wacce sojoji su ka jagoranta, sun shiga har fadar firayim ministan Abdalla Hamdok sun kama shi
  • Ganin rikici zai iya barkewa ya janyo su ka sanya dokoki tsaurara guda 3, ciki har da dakatar da duk wata kafar sadarwa a kasar
  • Sannan sun dakatar da duk wata hanyar zuwa Khartoum, babban birnin jihar kuma sojojin sun hana ababen hawa da mutane ketare har gadojin hanyar

Sudan - Sakamakon barkewar guguwar juyin mulki a kasar Sudan da ke nahiyar Afirka, manyan sojoji sun jagoranci juyin mulki inda su ka je har fadar Firayim ministan kasar kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Bisa ruwayar Legit.ng, sun isa fadar ta sa da ke Khartoum inda su ka kama PM Abdalla Hamdok.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Sudan: Tsauraran matakai 3 da sojoji su ka dauka bayan kama Firayim minista Hamdok
Sudan: Tsauraran matakai 3 da sojoji su ka dauka bayan kama Firayim minista Hamdok. Hoto: Abdalla Hamdok
Asali: Facebook

Bayan kama Hamdok, sojoji da wasu ministocin sa da ke babban birnin su ka dauki tsauraran matakai 3 don dakatar da wani rikici da ka iya faruwa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng ta samu damar tattaro matakan guda 3:

1. Sun dakatar da duk wasu hanyoyin sadarwa a kasar

Dakatar da hanyoyin sadarwa zai dakatar da yaduwar labarai sannan gidajen jaridu da talabijin za su kasance cikin duhu.

Hakan ya sa sojoji su ka dakatar don kada wani labari daga Khartoum ya yadu zuwa wani wurin na daban.

2. Sun dakatar da titinan da za su kai mutane Khartoum

Sojojin har ila yau sun dakatar da duk wasu titina da za su iya kai mutum fadar shugaban kasar inda Hamdok ya ke a daure cikin babban birnin kasar, Khartoum.

Hakan zai ba su damar hana duk wata damar da za ta taimaka wurin ceto Hamdok da ga hannun su idan har su ka ci nasarar juyin mulkin.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Sojojin Sudan sun saka dokar ta baci, sun damke shugabannin farar hula

3. Sojoji sun saka shinge a gadoji

Sojoji sun san ya shinge a gadoji ta yadda daga masu tafiya a kasa har masu ababen hawa ba za su iya wucewa ta gadojin da ke babban birnin ba.

Kamar yadda wakilin Al-Jazeera ya bayyana cewa:

“Sojoji sun dakatar da duk wasu hanyoyi da za su kai mutum Khartoum. Mun ga sojoji su na tare da titina inda su ka ce an ba su umarnin yin hakan ne.”
“Sun ce an hana shiga Khartoum. Kuma hakan abin tsoro ne don duk wasu ma’aikatun gwamnati a can su ke har fadar shugaban kasar da ofisoshin ministocin duk su na can.”

Dama wannan ba shi ne karo na farko da sojoji su ka taba yunkurin juyin mulki a kasar ba.

Sun taba yunkuri tun watan Satumban shekaru 2 da su ka wuce, lokacin mulkin Omar Al-Bashir wanda Abdallah Hamdok ya gada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel