Gwamnatin Eswatini ta kafa dokar hana yan ƙasa amfani da dandalin Facebook, ta faɗi dalili

Gwamnatin Eswatini ta kafa dokar hana yan ƙasa amfani da dandalin Facebook, ta faɗi dalili

  • Gwamnatin ƙasar Eswatini ta ɗauki matakin kafa dokar hana amfani da shafin Facbook ga yan ƙasarta
  • Rahotanni sun nuna cewa tuni gwamnatin ta umarci kamfanin MTN dake aiki a ƙasar ya hana hawa dandalin sada zumunta Facebook
  • Eswatini ta kafa wannan dokar ne bisa zargin shafin da yaɗa labarun dake ingiza wutar zanga-zangar da ake yi a ƙasar

Eswatini - Gwamnatin ƙasar Eswatini ta sanar da ɗaukar matakin dakatar da amfani dandalin sada zumunta na Facebook a faɗin ƙasar.

BBC Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin ta baiwa kamfanin sadarwa na MTN dake aiki a ƙasar umarnin ya gaggauta dakatar da hawa Facebook ga yan ƙasar.

Idan baku manta ba makonni da dama da suka gabata, gwamnatin Najeriya ta sanar da dakatar da amfanin da shafin Tuwita.

Kara karanta wannan

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

Dandalin Facebook
Gwamnatin Eswatini ta kafa dokar hana yan ƙasa amfani da dandalin Facebook, ta faɗi dalili Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Har zuwa yanzun ana cigaba da tattaunawa tsakanin gwamnati da kamfanin Tuwita domin sasanta wa da kuma dawo da aikin dandalin a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa Eswatini ta ɗauki wannan matakin?

Gwamnatin ƙasar ta bayyana cewa ta ɗauki wannan matakin ne a ƙoƙarin da take na shawo kan yan zanga-zangar rajin kare demokaraɗiyya.

Rahoto ya nuna cewa mutanen sun kwashe watanni suna gudanar da wannan zanga-zanga domin nuna kin amincewa da mulkin Mulukiyya.

Saboda haka ne gwamnatin ta ɗauki wannan matakin, domin tana zargin shafin na Facebook yana taimakawa wajen rura wutar zanga-zangar da irin labaran da yake yaɗawa.

Shin kamfanin MTN ya aiwatar da umarnin Gwamnati?

Kamfani sadarwa na MTN ya aikewa yan ƙasar da sakon karta kwana yana mai sanar da su matakin gwamnatin ƙasar ta ɗauka.

A wani labarin na daban kuma kun ji cewa a Najeriya, gwamnan Kano ya sha alwashin bude sabuwar jami'a a jiharsa

Kara karanta wannan

Nasarar jam'iyyar PDP na hannun yan Najeriya a zaɓen 2023, Inji Atiku

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da kiran da ake masa na ɗaga matsayin kwalejin Sa'adatu Rimi zuwa jami'a.

Freedom Radio ta ruwaito cewa kwalejin ta jima tana miƙa ƙoƙon bararta ga gwamna Ganduje kan ya maida ita matsayin jami'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel