Abdullahi Abubakar
7253 articles published since 28 Afi 2023
7253 articles published since 28 Afi 2023
Fusatattun matasa sun korar 'yan kasuwar Hausawa a Ekpoma, Gwamna Okpebholo ya yi Allah-wadai da harin. 'Yan sanda sun ceto mutane tara daga masu garkuwa.
Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu yayin da majalisar dokoki ke ci gaba da yunkurin tsige shi daga mulki.
Wani bidiyo da yan jaridu suka gani ya tabbatar da kashe ‘yan ta’adda da lalata maboyarsu a Sokoto, yayin hare-haren sama na Amurka a ƙarshen Disambar 2025.
Rahotanni sun ce a yammacin jiya, yayin taron Maulud a Yanshantuna, Makera, Dutsin-Ma, ‘yan bindiga sun kewaye jama’a, sun kwace wayoyi, kuɗi, sun sace shagon caji.
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya je Faransa domin ganawa da Shugaba Bola Tinubu kwanaki biyar bayan haduwa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a jihar.
Gwamnatin tarayya na shirin samun N5.4bn daga alhazan Najeriya ta hanyar kudin hidima na 2% don Hajjin 2026, IHR na neman bayyana hanyoyin amfani da kudin.
Jam’iyyar APC ta bayyana kwarin gwiwar lashe zaɓen 2027 bisa tsari mai ƙarfi da nasarorin gwamnati, tana karɓuwa daga ’yan kasa da ƙaruwa mambobinta a faɗin ƙasar.
Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje, ya dawo Najeriya daga Dubai, yana shirin karfafa hadin kai da rajistar mambobi ta intanet a fadin kasa.
Attajiri a Najeriya, Abdulsamad Rabiu ya taya kungiyar Super Eagles murnar doke Algeria inda ya ba su kyautar $500,000 domin karfafa musu guiwa a gasar AFCON.
Abdullahi Abubakar
Samu kari