Abdullahi Abubakar
7273 articles published since 28 Afi 2023
7273 articles published since 28 Afi 2023
Malamin addinin Kirista, Fasto Elijah Ayodele ya gargadi Bola Tinubu kan zargin sauya mataimakinsa, Kashim Shettima kamar yadda ake yawan yadawa kafin 2027.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa tsohon gwamnan soja na Plateau kuma Sanata da ya wakilci Adamawa ta Arewa, Kanal Muhammad Mana, ya rasu.
Bayan korafe-korafe ya yi yawa kan kisan masallata a jihar Katsina, Gwamnatin ta yi alkawarin cafke wadanda suka kai mummunan hari kan masu ibada.
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bukaci 'yan majalisar dokoki su mara wa Gwamna Ahmed Usman Ododo baya, domin ci gaban jihar gaba ɗaya.
Hafsan tsaro, Janar Christopher Musa ya nuna damuwa kan samun sojoji da ba su da kwarewar aiki, ya ce rundunar tana daukar tsauraran matakai wajen daukar ma’aikata.
Rundunar sojojin Najeriya ta yi nasara cafke fitaccen ɗan ta’adda da ya addabi jihohin Kaduna da kuma Plateau, Adamu Buba, wanda aka fi sani da ‘Mai Pankshin’.
Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom, ya halarci wani taro tare mutane masu halittar zabiya inda ya bayyana yadda aka yi masa ba’a yayin da yake kamfe na neman takara.
Yayin da aka kulla alaka tsananin Najeriya da Isra'ila, malaman Musulmi a Ibadan sun gudanar da zanga-zangar lumana, suna adawa da hakan a Ibadan da ke Oyo.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce kasar tana samun ci gaba sosai kuma yana rage matsaloli a karkashin shugabancinsa na shekaru biyu da ya yi.
Abdullahi Abubakar
Samu kari