Buhari ya warewa Majalisar Najeriya N234bn a 2022, kaso mafi tsoka a tarihin kasafin kudi

Buhari ya warewa Majalisar Najeriya N234bn a 2022, kaso mafi tsoka a tarihin kasafin kudi

  • ‘Yan Majalisar Tarayya za su batar da sama da Naira biliyan 230 a shekara mai zuwa
  • Kudin da aka ware wa majalisar shi ne kusan kaso mafi tsoka da aka taba gani a tarihi
  • Daga cikin wadannan kudi, akwai Naira biliyan 100 da aka ware na ayyukan mazabu

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kasafin Naira biliyan 234 a matsayin abin da ‘yan majalisar tarayya za su kashe a shekarar 2022 mai zuwa.

The Cable tace wannan ne kaso mafi tsoka da gwamnatin tarayya ta ware wa majalisa tun 2016. Amma da alamu ba a taba kashe irin wadannan kudin ba.

Naira biliyan 134 za a ba majalisa kai-tsaye daga cikin kasafin kudin shekarar badi. Bayan haka akwai Naira biliyan 100 da aka ware ayi ayyukan mazabu.

Read also

EFCC ta gurfanar da Yarima a gaban kotu kan badakalar N35.5m

Kudin da ‘yan majalisar wakilan tarayya da Sanatocin kasar za su batar a 2022 ya karu da Naira biliyan shida a kan abin da aka ware masu a shekarar 2021.

Rahoton yace Naira biliyan 128 aka ware wa majalisar tarayya a 2021. Sauran wadanda za a ba kudinsu kai tsaye sun hada da; NJC, PCC, NHRC, INCE da UBCE.

Ragowar su ne: NDDC, NASENI, da NEDC. Kusan an kara wa dukkaninsu kasonsu a kasafin badi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan Majalisar Najeriya
Shugaba Buhari a gaban 'Yan Majalisa Hoto: www.sunnewsonline.com
Source: UGC

Irin kudin da Majalisa ta ke samu

Har ila yau a cikin karin kasafin kudin shekarar bana da shugaban kasa ya aika wa majalisa, ‘yan majalisar sun amince a kara ware masu Naira biliyan daya.

Mai girma Muhammadu Buhari ya amince da wannan kari, kuma ya sa hannu. Tribune tace za a yi amfani da kudin wajen yi wa tsarin mulki garambawul.

Read also

Kano: Ganduje ya aike da Ƙarin N33.8bn kan kasafin kudin 2021 gaban majalisa

A 2021, abin da gwamnatin tarayya tayi wa majalisa kasafi shi ne Naira biliyan 125. Da kundin kasafin ya shiga hannunsu, sun kara kusan Naira biliyan 10.

Tsoron da mutane suke yi

Babu wanda ya san abin da kasafin kudin majalisa ya kunsa, baya ga cewa an san za a batar da Naira biliyan 134 wajen biyan albashi, alawus da kuma gudanarwa.

Ana tsoro wannan karo ‘yan majalisar na iya kara adadin kudin daga Naira biliyan 134, ya kara yin sama. Hakan na zuwa ne a lokacin da ake neman rage facaka.

An bada kwangiloli 800 a watanni 70

A makon nan ne aka ji cewa majalisar zartarwa ta kasa watau FEC ta amince da kwangiloli, manufofi da tsare-tsare sama da 1, 400 a mulkin Muhammadu Buhari.

A wa’adin Shugaba Buhari na biyun nan, Majalisar FEC ta yi taro sama da 50. Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya fitar da wadannan alkaluma.

Read also

Gwamna El-Rufai ya gabatar da kasafin kudin 2022 ga majalisar dokokin Kaduna

Source: Legit

Online view pixel