Duka Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun maka Gwamnatin Buhari a gaban kotun koli

Duka Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun maka Gwamnatin Buhari a gaban kotun koli

  • Ana rigima tsakanin Gwamnonin Jihohi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Gwamnoni sun kai karar Gwamnatin Tarayya a kan doka mai cikakken ido ta 10
  • Lauyoyin Gwamnonin Jihohi suna ikirarin dokar #10 ta ci karo da dokar Najeriya

Abuja - Manyan lauyoyin gwamnatocin jihohi sun shigar da kara a kotun koli, suna kalubalantar doka mai cin gashinta ta 10 da Muhammadu Buhari ya kawo.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa jihohi suna neman kotu ta raba gardama a kan hallacin wannan doka da ta ba majalisa da kotun jihohi gashin kansu.

Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun maka Gwamnatin Buhari a gaban kotun koli
Duka Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun maka Gwamnatin Buhari a gaban kotun koli. Hoto: Premium Times
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnatocin jihohin suna ganin cewa gwamnoni ya kamata su rika daukar dawainiyar kotunansu.

Read also

Kano: Babbar kotu ta umarci Ganduje ya biya Jaafar Jafaar N800,000

Gwamnoni sun yi imani cewa nauyin gwamnatin tarayya ne ta dauki hidimar albashi da sauran hakkokin manyan kotun tarayya, na shari’a da na daukaka kara.

Suna cewa dokar ta saba wa sassa na 6(5), 81(3) da layi na 21(3) na kundin tsarin mulkin kasa.

Rahoton da aka fitar dazu yace gwamnoni suna ikirarin dokar mai cikakken iko da shugaban kasa ya kawo ta ci karo da kundin tsarin mulki da dokar kasa.

Doka ta #10 ta ba Akanta-Janar damar ya cire kason kotunan jihohi daga kudin gwamnatin tarayya, ya tura masu rabonsu kai-tsaye ta majalisar shari’a, NJC.

Jaridar ta rahoto cewa gwamnatin tarayya ta bakin AGF ta maida martani a kotu, tana cewa aikinta ne ta biya Alkalai duk wasu albashi da alawus din aikinsu.

Ministan shari’a, Abubakar Malami yace ba daidai bane gwamnonin jihohi su nemi gwamnatin tarayya ta biya su kudin da ta kashe a kan kotun da ke jihohinsu.

Read also

Gwamnatin Buhari za ta fara biyan daliban digiri da NCE kudin kashewa

“Tun Mayun 1999, gwamnatin tarayya take daukar nauyin bangaren shari’a kamar yadda sashe na 84 na kudin tsarin mulki ya tanada.” - Abubakar Malami.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel