Kano: Babbar kotu ta umarci Ganduje ya biya Jaafar Jafaar N800,000

Kano: Babbar kotu ta umarci Ganduje ya biya Jaafar Jafaar N800,000

  • A ranar Litinin, Babbar kotun jihar Kano wacce Alkali S.B Namalam ya yi shari’a ta bukaci Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya biya Jaafar Jaafar
  • Kamar yadda alkalin ya bukata, Ganduje zai biya mai jaridar Daily Nigerian N800,000 sakamakon kashe-kashen kudade da ya sa dan jaridar ya yi
  • Duk hakan sanadiyyar rikicin dan jaridar ya saki wani bidiyon gwamnan ne wanda yake kalmashe daloli a babbar rigar sa, rikicin da ya ki karewa

Kano - Babbar kotun jihar Kano bisa alkalancin Justice S.B Namalam a ranar Litinin ta bukaci gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya biya mai jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar N800,000 bisa kashe-kashen kudaden da ya janyo ma sa na kotu sanadiyyar rikicin bidiyon dala.

Alkalin ya ce kotu ba za ta saurari Ganduje ba matsawar bai biya shi N800,000 ba kafin zagayowar ranar da kotu zata ci gaba da sauraron karar kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Read also

An tsaurara tsaro yayinda Shugaba Buhari ke shirin gabatar da kasafin kudin 2022 yau

Kano: Babbar kotu ta umarci Ganduje ya biya Jaafar Jafaar N800,000 ko kuma...
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da Jaafar Jaafar. Hoto: Daily Nigerian
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lauyar Ganduje, Lydia Oyewo ta bai wa kotu hakuri kuma ta yi alkawarin tattaunawa da Ganduje don biyan kudin kamar yadda alkalin ya bayar da umarni tun ranar 6 ga watan Augustan 2021.

Tushen shari’ar

Ganduje ya maka Jaafar Jaafar da jaridar Daily Nigerian kara a kotu bayan sakin wani bidiyon sa wanda ya nuna gwamnan ya na kalmashe daloli a cikin aljihun sa yayin da wani da ake zargin dan kwangila ne yake mika masa.

Gwamnan ta lauyan sa ya bukaci Jaafar ya biya shi N3,000,000,000 sakamakon bata ma sa suna da ya yi.

Ganduje ya tura korafin sa ta lauyan sa Offiong Offiong, SAN a ranar 28 ga watan Yuni ya na bukatar kotu ta dakatar da karar, daga baya kuma ya kara kai kara babbar kotun Abuja duk da kotun Kano tana kan hukunci.

Read also

Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

Lauyoyin Jaafar da Penlight Media Limited, U.U Etang da M.B. Dan’Azumi duk ba su hana dakatar da shari’ar ba sai dai sun bukaci ya biya su N400,000,000 idan hakan zai tabbata.

Kotu ta ba Ganduje umarnin biyan Jaafar da Daily Nigerian N400,000 ko wannen su.

Har yanzu dai Ganduje be yi abinda kotu ta umarci ya yi ba daga nan kotu ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Nuwamba.

Penlight Media sun mayar da lauyan su daga Dr. Dan’Azumi zuwa Abdul Mohammed, SAN.

Mutane su na barazanar halaka ni, Likitan Najeriya da ya buɗe wurin gwajin DNA tare da yin rahusa na kashi 70

A wani labarin daban, wani likita wanda ya bude wurin gwajin kwayoyin halitta na DNA a anguwarsu ya bayyana yadda wasu mutane suke barazanar halaka shi a shafin sa na dandalin sada zumunta sakamakon zargin zai zama kalubale ga aurensu.

Read also

Bishiya mai shekaru 100 ta fadi kan mutane, ta hallaka jariri da mahaifiyarsa

Kamar yadda Pulse Nigeria ta ruwaito, likitan mai suna Dr Penking ya bayyana cewa zai bude wurin gwajin DNA din a jihar Legas ne kuma zai samar da rahusar kaso 75 bisa dari a watan Oktoba.

Mutane da dama sun yarda da cewa wannan rahusar za ta bai wa maza da yawa damar tabbatar wa idan su ne iyayen yaran su na hakika, hakan ya kada ruwan cikin jama’a.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel