Bidiyon Yadda Wani Mutum Ya Haukacewa Banki Saboda an Cire Kudinsa Daga Asusu

Bidiyon Yadda Wani Mutum Ya Haukacewa Banki Saboda an Cire Kudinsa Daga Asusu

  • Wani dan Najeriya ya dumfari banki tare da tada kura bisa zargin an zare masa kudi ba bisa wata ka'ida ba
  • A wani bidiyon da aka yada a kafar TikTik, mutumin ya cire rigarsa, ya zauna dirsham a kan dandamalin banki, lamarin da ya ba wasu mamaki
  • Mutane da dama sun yi dandazo a sashen sharhin bidiyon, sun bayyana martaninsu tare da kira ga bankin su biya wa mutumin bukatarsa

Wani bidiyon dan Najeriya da ya tada zaman lafiyan banki ya yadu a kafar sada zumunta, an ga lokacin da yake bayyana bacin ransa.

Ba a dai san dalilin da yasa mutumin ya girgiza bankin ba, amma wasu na tunanin ba zai rasa nasaba da cire masa kudi daga asusunsa.

Kara karanta wannan

Bera ya yi batan hanya a ofishin NDLEA, ya fada dakin wiwi, abin da ya yi ya ba da mamaki

A bidiyon da aka yada gajere, mutumin ya cire rigarsa, ya zauna dirsham kan dandamalin banki inda yake caccakar ma'aikatan da bankin su kuwa suna kallonta.

Wani mutum ya birkice a banki saboda an cire masa kudi a asusu
Bidiyon Yadda Wani Mutum Ya Haukacewa Banki Saboda an Cire Kudinsa Daga Asusu | Hoto: TikTok/@arikeoladayo5
Asali: UGC

Duk kokarin da mutumin ke yi a banza, yayin da yake ci gaba da daga murya yana azalzalar ma'aikatan bankin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

Bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta ya jawo cece-kucen al'umma, mutane da dama sun yi hasashen abin da ke faruwa.

Wasu na tona irin laifukan da ma'aikatan banki ke yi, wasu kuwa na ganin laifin kwastomomin da ke amsa kiran 'yan damfara.

Ga dai abin da suke fadi:

@tzwhyte_official yace:

"Wayyo! Kada ka dauki kiran 'yan damafa, kada ka ba da bayananka a lokacin da aka kira ka, ka dai ji ko. Ka ga dai sakamako.

@rahmatolatundunbi yace:

Kara karanta wannan

Matashi Ya Sheke Mahaifinsa Har Lahira Bayan Ya Rafka Maka Itace

"Wannan ne kadai yaren da suke fahimta."

@usmanadam847 yace:

"Duk da dai rayuwa na da wahala, amma ina son kasa ta."

@user6430810072171 yace:

"Ina jiran ranan da banki na zai haukace ne, kuma na tafi yin korafi sannan su raina ni, na rantse za su gane."

Bidiyon Beran da Ya Shiga Dakin Ajiye Tabar Wiwi a Ofishin NDLEA Ya Ba da Mamaki

A wani labarin, wani bera ya yi batan hanya, ya fada wurin da bai kamata ya tsinci kansa ba a ofishin hukumar yaki da hana shan miyagun kwayoyi ta NDLEA.

Hukumar ta yada bidiyo na yadda beran ke fagauniya bayan shakar kayan shaye-shaye da hukumar ke kwatowa a kai ma'ajiyar hukumar.

Bidiyon da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya fitar a ranar Litinin a shafinsa na LinkedIn ya nuna irin dabi'un da beran ke yi da ba a saba gani ba.

Kara karanta wannan

Hana Sallar Juma'a: Musulmi Sun Fara Zuwa Bankin Polaris Suna Rufe Asusun Ajiyarsu

Asali: Legit.ng

Online view pixel