Jerin Sabbin Matakai 8 da Gwamnatin Jihar Kaduna ta Dauka don Dakile Ayyukan Ta’addanci

Jerin Sabbin Matakai 8 da Gwamnatin Jihar Kaduna ta Dauka don Dakile Ayyukan Ta’addanci

Gwamnatin jihar Kaduna ta bi sahun makwabtanta na Kastina da Zamfara wajen kafa sabbin dokoki don dakile matsalar tsaro da ya addabi jihar.

Jihohin Arewa maso yammacin Najeriya na fama da matsanancin rikicin yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Gwamnan jihar da kansa ya jera sabbin dokoki domin ganin an kawo karshen wannan lamari a jawabin da ya saki a shafinsa na Facebook.

El-Rufa'i yace:

Muna amfani da wannan kafa ta Facebook domin sanar da al'umma matakan da muka ɗauka a ƙoƙarin da muke yi na daƙile ayyukan ta'addanci kamar yadda jami'an tsaro suka ba mu shawara.

Jerin Sabbin Matakai 8 da Gwamnatin Jihar Kaduna ta Dauka don Dakile Ayyukan Ta’addanci
Jerin Sabbin Matakai 8 da Gwamnatin Jihar Kaduna ta Dauka don Dakile Ayyukan Ta’addanci Hoto: Governor Kaduna
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Jihar Niger: Mayaƙan Boko Haram sun ratsa mazaɓu 8 cikin 25, Shugaban Ƙaramar Hukuma

Waɗannan matakai sun haɗa da:

1. Rufe layukan sadarwa a wasu yankunan jihar

2. Hana amfani da babura (mashin) a duk fadin jihar har na tsawon wata uku.

3. Hana mallakar makamai

4. Hana amfani da Keke Napep bayan karfe bakwai na yamma zuwa karfe shida na safe, sannan kuma an hana su amfani da labule.

5. Hana sayar da man fetur a jarakuna a Karamar Hukumar Birnin Gwari da Giwa da Chikun da Igabi da Kachia da Kagarko da Kajuru.

6. Hana safarar gawayi da itace

7. Hana safarar dabobbi; shigowa da fita da su wajen jihar

8. Hana cin kasuwannin sati-sati ko mako-mako a ƙananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa da Chikun da Igabi da Kasuwar Kawo da ke Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa

Gwamnan ya kara da cewa yana bayar da haƙuri na halin ƙunci da al’umma za su shiga saboda waɗannan matakan.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya yi iƙirarin wasu manya sun daƙo hayar masu kisa daga ƙasar waje su kashe shi

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng