Hotunan auren ɗan gwamnan Jihar Jigawa da zuƙeƙiyar budurwarsa da suka hadu a Snapchat

Hotunan auren ɗan gwamnan Jihar Jigawa da zuƙeƙiyar budurwarsa da suka hadu a Snapchat

  • Dan gwamna Mohammed Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya angwance da budurwar sa, Affiya Sadiq Umar a ranar 11 ga watan Satumban 2021
  • An samu rahotanni akan yadda ya hadu da tsaleliyar budurwar a kafar sada zumuntar zamani ta Snapchat
  • Kamar yadda mai hoton su ya bayyana a shafin sa na Instagram ya ce soyayyar ta fara ne bayan Abdul ya yi tsokaci akan hoton Affiya

Jihar Jigawa - Dan gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya zama angon zankadediyar budurwar sa a ranar 11 ga watan Satumba bayan haduwar su a wata kafar sada zumuntar zamani ta Snapchat.

'Dan gwamnan Jihar Jigawa ya yi wuf da zuƙeƙiyar budurwarsa da suka hadu a Snapchat
Hotunan dan gwamnan Jihar Jigawa da amaryarsa. Hoto: Atilary Studio
Source: Instagram

Kamar yadda LIB ta ruwaito, mai hoton bikin su, Atilary ne ya wallafa hakan a shafin sa na Instagram a ranar Talata, 21 ga watan Satumba, inda ya bayyana cewa soyayyar ta su ta fara ne a kafar sada zumunta bayan Abdul ya yi tsokaci akan hoton ta.

Read also

Gagarumin sako zuwa Kudu maso Gabas: Ku rungumi APC ko ku rasa dama a 2023, Tsohon dan majalisa yayi gargadi

'Dan gwamnan Jihar Jigawa ya yi wuf da zuƙeƙiyar budurwarsa da suka hadu a Snapchat
'Dan gwamnan Jihar Jigawa ya auri zuƙeƙiyar budurwarsa da suka hadu a Snapchat. Hoto: Atilary Studios
Source: Instagram

'Dan gwamnan Jihar Jigawa ya yi wuf da zuƙeƙiyar budurwarsa da suka hadu a Snapchat
'Dan gwamnan Jihar Jigawa ya yi wuf da zuƙeƙiyar budurwarsa da suka hadu a Snapchat. Hoto: Atilary Studio
Source: Instagram

Waye ya ce soyayyar kafar sada zumunta karya ce?

Kamar yadda mai hoton ya wallafa:

“Waye ya ce soyayyar kafar sada zumuntar zamani karya ce? Soyayyar ta fara ne tun bayan Abdul ya ga hoton ta a Snapchat ya rude ya yi mata tsokaci da “cutie” ma’ana kyakkyawa. Kuma a ranar ya ce ya hadu da matar sa kuma ga shi ya tabbata.”

'Dan gwamnan Jihar Jigawa ya yi wuf da zuƙeƙiyar budurwarsa da suka hadu a Snapchat
Dan gwamnan jihar Jigawa ya auri budurwarsa da suka hadu a Snapchat. Hoto: Atilary Studio
Source: Instagram

LIB ta ruwaito yadda mai hoton ya wallafa kyawawan hotunan su masu daukar hankalin mai kallo.

Saurayina da muka yi shekaru 4 tare ya yi wuf da ƙawata da suka haɗu cikin watanni 6, Budurwa

A wani labarin akasin wannan, kun ji cewa wata budurwa ta garzaya dandalin sada zumunta na zamani inda ta bayyana yadda saurayin ta ya yaudare ta, rahoton LIB.

Read also

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

A cewar ta ya yanke shawarar auren wata daban wacce ya hadu da ita ta wurin budurwar sa cikin watanni 6 kamar yadda LIB ta ruwaito

Budurwar, wacce ‘yar kasar Afrika ta Kudu ce ta bayyana yadda duk da sun kwashe shekaru 4 kwatsam ya juya mata baya.

Source: Legit

Online view pixel