Saurayina da muka yi shekaru 4 tare ya yi wuf da ƙawata da suka haɗu cikin watanni 6, Budurwa
- Wata budurwa ta bayyana yadda saurayin ta da suka kwashe shekaru hudu tare ya yaudare ta
- A cewar ta duk da kwashe shekaru hudun da suka yi su na soyayya wata can daban zai aura
- Kamar yadda ta bayyana, ya san wacce zai aura ne ta wurin ta kuma watanni 6 kenan da haduwar su
Afirka ta Kudu - Cikin takaici da cizon yatsa wata budurwa ta garzaya dandalin sada zumunta na zamani inda ta bayyana yadda saurayin ta ya yaudare ta, rahoton LIB.
A cewar ta ya yanke shawarar auren wata daban wacce ya hadu da ita ta wurin budurwar sa cikin watanni 6 kamar yadda LIB ta ruwaito
Budurwar ta ce sun kwashe shekaru hudu su na kwasar soyayya ashe duk yaudarar ta yake shirin yi.
Budurwar, wacce ‘yar kasar Afrika ta Kudu ce ta bayyana yadda duk da sun kwashe shekaru 4 kwatsam ya juya mata baya.
Kamar yadda ta wallafa a shafinta na dandalin sada zumunta:
“Saurayi na wanda muka kwashe shekaru 4 muna soyayya zai auri wata da ya hadu da ita ta hanya ta cikin watanni shida.”
Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyin su game da lamarin, wasu suna ganin saurayin ba shi da laifi yayin da wasu kuma suke ganin ya ci amana.
Jigawa: Hotunan Auren Yaya Da Ƙanwa Da Kotun Shari’ar Musulunci Ta Aurar Da Su Duk Da Ƙin Amincewar Mahaifin Su
A wani labarin na daban, wata babban kotun Shari'a a ƙaramar hukumar Hadejia na Jihar Jigawa, a ranar Alhamis, ta aurar da wasu mata biyu ƴaƴa da ƙanwa, Premium Times ta ruwaito.
An aurar da matan biyu ne bayan mahaifinsu, Mallam Abdullahi Malammmadori, ya ƙi aurar da su duk da wa'adin kwanaki 30 da kotun ta bashi amma bai aurar da su ba.
Shugaban wata gidauniya na taimakon mata, marayu da marasa galihu, Fatima Kailanini, ta yi ƙarar Mr Malammadori kan ƙin aurar da Khadijat da Hafsat Abdullahi duk da sun fito da waɗanda suke so.
Shugaban wata gidauniya na taimakon mata, marayu da marasa galihu, Fatima Kailanini, ta yi ƙarar Mr Malammadori kan ƙin aurar da Khadijat da Hafsat Abdullahi duk da sun fito da waɗanda suke so.
Asali: Legit.ng