Karya Fani-Kayode ya sharara, babu hannunsa a sauya-sheka ta daga PDP inji Gwamnan APC

Karya Fani-Kayode ya sharara, babu hannunsa a sauya-sheka ta daga PDP inji Gwamnan APC

  • David Umahi ya maida martani a kan wasu kalamai da Femi Fani-Kayode ya yi jiya
  • An ji Fani-Kayode yana cewa ya taimaka wajen karkato da ra’ayin gwamnonin PDP
  • Umahi yace Fani-Kayode bai san lokacin da ya zabi ya sauya-sheka zuwa APC ba

Ebonyi - Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya bukaci Femi Fani Kayode ya janye kalaman da ya yi bayan sauya-shekarsa zuwa jam’iyyar APC a jiya.

An rahoto tsohon Ministan harkokin jirgin sama, Cif Femi Fani Kayode yana cewa ya taka rawar gani wajen jawo wasu gwamnoni daga PDP zuwa APC.

Jaridar Daily Trust ta rahoto daya daga cikin sababbin shiga jam’iyyar APC yana maida martani, inda yace ya kamata Fani-Kayode ya janye kalamansa.

Kara karanta wannan

Fani-Kayode: Abin da ya sa aka ji ni a APC duk da na yi wa Shugaba Buhari da wasu ta-tas a baya

Ka janye kalaman ka, karya ne - Umahi

“Ina tunanin ya kamata ya janye kalamansa, aboki na ne, amma rainin hankali a wurina da sauran gwamnoni.”
“Mutumin nan bai san lokacin da na sauya-sheka ba, ya kawo mani ziyara, kuma yace shi ma zai shigo (jam’iyyar APC) tare da mu da sauran gwamnoni.”

Dave Umahi yace a matsayinsa na shugaban gwamnonin jihohin kudu maso gabashin Najeriya, Fani-Kayode bai da ta-cewa a kan matakin da zai dauka.

Karya Fani-Kayode
Umahi da Fani Kayode Hoto; pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

“Ya za ayi wanda yake jam’iyyar PDP ya taka rawar gani wajen sauya-sheka ta. Gwamna guda! Ba karamin gwamna ba fa, gwamnan da ya kware a aiki.”
“Dole ya lashe amansa. Bai cikin wadanda aka zauna da su lokacin da zan tashi. Na bar kudu maso gabas, na hade da gwamnatin tarayya da ke kan mulki.”

Kara karanta wannan

Mayaudarin dan Oduduwa: Sheikh Ahmad Gumi ya caccaki Fani Kayode bayan komawa APC

“Wani ya zo yana cewa ya yi kokari wajen tafiya ta, ina shugaban gwamnonin kudu maso gabas, kamar rainin hankali ne a wuri na. Ya janye kalamansa.”

Punch tace Gwamnonin da suka bar PDP zuwa APC bayan Dave Umahi su ne; Ben Ayade da Bello Matawalle.

Femi Fani-Kayode: Dalilin dawo wa APC

A jiya aka ji Femi Fani-Kayode ya na kare kan shi bayan komawarsa jam’iyyar APC inda yace a da ban san Buhari amma yanzu ya gane shi, kuma APC ta canza.

Da yake magana a wani shirin Channels TV, Cif Femi Fani-Kayode ya fadi babban dalilin sa na sauya-sheka, sannan yace ba zai tanka PDP ba sai sun taba shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel