Hotunan takardun da ƴan ISWAP suka raba wa mutane a Borno suna gargaɗinsu game da kai wa sojoji tsegumi

Hotunan takardun da ƴan ISWAP suka raba wa mutane a Borno suna gargaɗinsu game da kai wa sojoji tsegumi

  • Yan ta'addan kungiyar ISWAP sun raba wa wasu mutanen Borno takardu dauke da sako na gargadi
  • A cikin takardun, yan ta'addan sun gargadi mutanen garuruwan kan hada kai da sojoji ko kai musu bayanan sirri
  • Yan ta'addan sun shaidawa mutanen garuruwan cewa sojoji ne makiyansu ba yan ISWAP ba don haka su dena hada kai da su

Kungiyar ta'addanci ta Islamic States West African Province (ISWAP), tsagin Boko Haram ta gargadi wasu mazauna Borno, musamman wadanda ke rayuwa a wuraren da suke da iko game da bawa sojoji bayanai.

Yan ta'addan sun yi wannan gargadin ne cikin wasu takardu da suka raba wa mutane a wani yanayi mai kama da kasuwa a jihar Borno a cewar rahoto HumAngle.

Hotunan takardun da ƴan ISWAP suka raba wa mutane a Borno suna gargaɗinsu game da kai wa sojoji tsegumi
Dan ISWAP na mika wa mutanen Borno takarda mai dauke da sako. Hoto. HumAngle
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

ISWAP ta yi ikirarin sheke sojin Najeriya 10, sace makamai da alburusai a Rann

Hotunan takardun da ƴan ISWAP suka raba wa mutane a Borno suna gargaɗinsu game da kai wa sojoji tsegumi
Mayakin ISWAP yayin da ya ke mika wa wani takardan gargadi. Hoto: HumAngle
Asali: Facebook

Kamar yadda ya ke a hotunan da aka fitar, daya dga cikin yan ta'addan na ISWAP yana mika wa wani mutum mai kama da direban tasi takardar.

An yi wa takardar lakabi da 'Sako daga dakarun daular musulunci zuwa ga mutanen sabon gari.'

Hotunan takardun da ƴan ISWAP suka raba wa mutane a Borno suna gargaɗinsu game da kai wa sojoji tsegumi
Takardar sako da ISWAP suka raba wa mutanen Borno. Hoto: HumAngle
Asali: Facebook

Yan ta'addan suna watsa farfaganda cewa Rundunar Sojojin Nigeria ne ta kore su daga gidajensu kuma sojojin ne makiyansu na gaskiya ba ISWAP ba.

Daya daga cikin sakonnin da ke takardun ya ce:

"Ba mune muka kore ku daga gidajen ku ba tunda farko, wadannan mutanen masu kiran kansu sojojin Nigeria ne suka kore ku, suka kashe ku, suna azzalumai."

'Yan ta'adda sun fara amfani da farfaganda don janyo hankalin kan mutanen Borno

A baya-bayan nan ISWAP ta koma amfani da farfaganda domin watsa sakonninta.

Yan ta'addan kuma suna bawa mutane tallafin kudi domin neman mutanen su cigaba da zama a karkashin daularsu.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun kwace Rann, sa'o'i bayan farmakin mayakan ISWAP

A baya bayan nan, SaharaReporters ta ruwaito cewa shugaban cibiyar adalci a addini da kabilanci a NIgeria, Kallamu Musa Ali Dikwa ya taba cewa Boko Haram ta karbi wasu sassan Borno ba tare da sojoji sun tanka musu ba.

Dikwa ya kuma ce yan ta'addan sun tare motocci a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu sun sace mutane ba tare da sojoji sun taka musu birki ba.

Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina

A wani labarin daban, kun ji cewa Yan bindiga sun sace dalibai da dama da malami guda daya a makarantar Islamiyya da ke kauyen Sakkai a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton na Daily Trust, an sace daliban ne yayin da suke daukan darrusa a harabar makarantar da yamma.

A halin yanzu ba a kammala tattaro bayannan yadda lamarin ya faru ba kuma ba a san inda aka tafi da wadanda aka sace din ba a lokacin hada wannan rahoton.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel