Sojoji ba su yi wa jiragen ruwa dauke da kaya ruwan bama-bamai ba, DHQ
- Hedkwatar tsaro ta musanta rahotanni jirgin sama na sojoji ya harbi wani jirgin ruwa da ke tafe da mutane da kuma kayan abinci
- An samu yaduwar rahotanni a ranar Juma’a cewa sojojin sama sun bude wa wani jirgin ruwa wanda yake dauke da kayan abinci wuta
- A ranar Litinin, darektan yada labaran soji, manjo janar Benjamin Sawyer ya saki wata takarda inda yace labarin kanzon kurege ne
FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta musanta rahotanni a kan yadda wani jirgin sama na sojoji ya bude wa wani jirgin ruwa da ya ke tafe da jama’a da kayan abinci tun daga Fatakwal zuwa Bonny wuta.
Daily Trust ta ruwaito cewa, an samu yaduwar rahotanni a ranar Juma’a cewa sojoji sun bude wa wani jirgin ruwa mai dauke da kayan abinci wuta tun daga Fatakwal zuwa Bonny.

Asali: UGC
A ranar Juma’a, darektan yada labaran soji, Manjo Janar Benjamin Sawyer ya saki takardar da ya musanta rahoton.
A cewarsa, bayan samun rahotan ne suka tura wani jirgin sama don kai dauki wuraren Cawthrone, Daily Trust ta ruwaito.
A cewarsa, jirgin ya ga wani jirgin satar man fetur wanda aka fi sani da “Cotonou Boat”.
An zargi jirgin wanda wasu jirage biyu suke biye da shi suna dauke da man fetur na sata a manyan dirarruka yana tafe wuraren jirgen OPDS da suke zagaye da su.
Bayan ganin jirgin ne sojoji suka yi harbi daya don dakatar da jiragen daga cigaba da tafiya. Sai jiragen suka bude wa sojoji wuta daga nan sojoji suka mayar da harbin.
Daga nan ne jirage biyun da suke raka jirgin satar man suka tsere suka bar “Contonou Boat” din wanda sojoji suka yi ta bude wa wuta.
Bayan nan ne jirgin sojojin ya bi sawun jiragen guda biyu amma bai samu nasarar ganinsu ba, yanzu haka ana cigaba da nemansu,” a cewarsa.
Kakakin sojin ya ce har yanzu sojoji suna cigaba da ayyuka cikin kwarewa da kuma bin duk abubuwan da doka ta tanadar.
Ya kara da cewa sojoji suna da alhakin kulawa da rayukan al’umma ne ba wai cutar da su ba.
Ya bukaci jama’a da su share duk wani labari na kanzon kurege da za su ji kuma su samar da labarai masu kyau wadanda za su taimaka wa sojoji wurin tsare lafiyarsu, dukiyoyinsu da kuma na gwamnati a bangaren kudu-kudu.
Buhari ya gana da shugaban NIS, ya bada sabon umarni kan iyakokin kasar nan
A wani labari na daban, Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, NIS, Muhammed Babandede, a ranar Juma'a ya yi bayani ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ayyukan NIS na kokarin tsare iyakokin kasar nan.
Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, a yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati a karshen taron sirri da yayi da shuagaban kasa, Babandede ya ce NIS ta kirkiro da sabbin tsare-tsare domin duba yanayin shige da fice bakin haure a kasar nan ba bisa ka'ida ba.
Kamar yadda yace, hukumar ta samu kayan aiki masu kyau domin taimaka wa wurin fallasa jama'ar da ke zama a kasar nan ba bisa ka'ida ba bayan hatimin shigowa kasar nan nasu ya gama aiki.
Asali: Legit.ng