Buhari ya gana da shugaban NIS, ya bada sabon umarni kan iyakokin kasar nan

Buhari ya gana da shugaban NIS, ya bada sabon umarni kan iyakokin kasar nan

  • Shugaban hukumar kula da shige da fice na kasa, Muhammed Babandede, ya samu yin ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Babandede ya sanar da manema labaran gidan gwamnati cewa shugaban kasa ya bukaci a tsananta tsaro a iyakokin kasar nan
  • Shugaban ya kara da cewa, hankali Buhari yana kan 'yan Najeriya domin ya ce bai yadda bakin haure su danne kasuwancin 'yan kasa ba

Aso Villa, Abuja - Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, NIS, Muhammed Babandede, a ranar Juma'a ya yi bayani ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ayyukan NIS na kokarin tsare iyakokin kasar nan.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, a yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati a karshen taron sirri da yayi da shuagaban kasa, Babandede ya ce NIS ta kirkiro da sabbin tsare-tsare domin duba yanayin shige da fice bakin haure a kasar nan ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Tattaunawa da Ortom: 'Yan jaridan Channels TV sun kwashe sa'o'i a hannun jami'an DSS

Buhari ya gana da shugaban NIS, ya bada sabon umarni kan iyakokin kasar nan
Buhari ya gana da shugaban NIS, ya bada sabon umarni kan iyakokin kasar nan. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Kamar yadda yace, hukumar ta samu kayan aiki masu kyau domin taimaka wa wurin fallasa jama'ar da ke zama a kasar nan ba bisa ka'ida ba bayan hatimin shigowa kasar nan nasu ya gama aiki.

Ya ce:

Na zo domin yi wa shugaban kasa bayani saboda ya bamu aiki tabbatar tsaro domin samun zaman lafiya tare da kwanciyar hankali a Najeriya.

Kamar yadda muka sani, NIS hukuma ce ta tsaro da ke da alhakin tsare iyakoki, a lokaci daya kuma tana bada gudumawa wurin saukake yin kasuwanci, Daily Nigerian ta ruwaito.

Don haka a yau na samu damar yi wa shugaban kasa bayani kan abinda muke yi kuma ya kara mana aiki ta hanyar sanar da mu abinda zamu yi domin tabbatar da tsaro.

Kara karanta wannan

Ka Daina Magana Ta Bakin Mataimaka, Yan Najeriya Na Bukatar Jin Muryarka, Sanatan APC Ga Buhari

Ya dace 'yan Najeriya su kara farin ciki ganin cewa iyakokin kasar nan za su kasance masu ingancin tsaro fiye da da. Kuma za mu tabbatar da cewa ba a dinga samun damar tsallake iyakokin ba ta yadda bai dace ba.
Dukkan jama'ar da ba 'yan kasa ba wadanda ke Najeriya, ya zama wajibi a kan mu mu dinga duba abinda suke yi da zai amfani kasar nan.

Ya bayyana cewa shugaban kasa ya daurawa hukumar alhakin tabbatar da cewa ba a hana 'yan Najeriya yin kasuwancinsu ta halastacciyar hanya ba kuma dole ne a baiwa ma'aikatansu kariya.

Kamar yadda ku ka sani, kowanne mutum yana shiga Najeriya ne da sharadi, ko dai yayi a kasuwanci ko ya kafa kasuwanci, amma ba wai su kwacewa 'yan Najeriya kasuwacinsu ba.
Don haka shugaban kasa ya daura mana alhakin tabbatar da cewa mun duba sosai mun tabbatar da cewa an baiwa gumin 'yan Najeriya kariya, tattalin arziki kariya, kuma ba mu bar bakin haure da suka shigo yin kasuwanci sun kwace ba.

Kara karanta wannan

Ya kamata sojoji su zage dantse: Buhari ya yi martani mai zafi kan harin NDA

Asali: Legit.ng

Online view pixel