Bauchi: 'Yan sanda sun yi ram da mutum 352 da ake zargi da garkuwa da mutane

Bauchi: 'Yan sanda sun yi ram da mutum 352 da ake zargi da garkuwa da mutane

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kwace bindigogi kirar AK-47 guda 25 da sauran miyagun makamai guda 6,460 cikin watanni 6 da suka gabata
  • Har ila yau, ta kama mutane 352 da ta ke zargin suna da hannu a ta’addanci 221 a ciki da wajen jihar cikin wadannan watannin
  • Jami’in hulda da jama'a na rundunar, Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan a wata takarda wacce ya bai wa manema labarai a ranar Juma’a

Bauchi - Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta ce jami’an ta sun kwace bindigogi kirar AK-47 guda 25 da sauran miyagun makamai guda 6,460 cikin watanni 6 da suka gabata.

Punch ta ruwaito cewa, ya kara da bayyana yadda suka kama wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne guda 352 wadanda suke da masaniya da laifuka 221 daban-daban cikin wannan lokaci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur, ta bayyana dalili

Jami’in hulda da jama’a, Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan a wata takarda wacce ya bai wa manema labarai a ranar Juma’a, inda yace tun daga watan Maris suke kamen har zuwa yanzu.

Bauchi: 'Yan sanda sun yi ram da mutum 352 da ake zargi da garkuwa da mutane
Bauchi: 'Yan sanda sun yi ram da mutum 352 da ake zargi da garkuwa da mutane. Hoto daga The Punch
Asali: Facebook

A cewarsa, jihar Bauchi tana daya daga cikin jihohin arewa maso gabas a kasar nan, kuma tana fama da matsalolin rashin tsaro kamar garkuwa da mutane, fashi da makami, satar shanu, ta’addanci, fyade da wasu munanan laifuka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Punch ta ruwaito, ya kara da cewa:

Domin kokarin ganin mun yi yaki da laifuka da ta’addanci a jihar, rundunar ‘yan sanda ta bazama wurin bin hanyoyi da salo na ganin ta kawo karshen wadannan matsalolin.

Yayin bayar da yawan mutanen da ake zargi da aikata laifuka, ya ce an kama mutane 115 wanda mutane 42 an kama su da laifin fashi da makamai ne, 69 kuma ana zarginsu da laifukan da suka danganci fyade.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Mun taba yi wa mutum 76 jana’iza a lokaci guda, babu wanda ya ji labari inji Sultan

Akwai 28 daga cikinsu da ake zarginsu da laifuka 18 da suka danganci garkuwa da mutane. An samu nasarar ceto mutane 15 daga hannun masu garkuwa da mutane.

Wakil ya kara da cewa, 66 daga cikinsu suna da hadi da laifukan kisa a fadin jihar sannan mutane 4 daga cikinsu suna da alaka da yunkurin kisa.

Ya bayyana yadda aka samu nasarar kwace miyagun makamai marasa lasisi wanda mutanen suka ajiye da sunan amfani da su wurin kare kawunansu, bindigogi 88 da sauran miyagun makamai 6,460 duk a cikin watanni 6.

Kamar yadda Punch ta ruwaito, ya ce 25 daga cikin bindigogin kirar AK-47 ne, sai wata bindigar toka, akwai wata AK-47 da suka hada da hannunsu, kananun bindigogi da sauran miyagun makamai.

Kano: An Saka Dokar Haramta Zancen Dare Tsakanin Samari Da Ƴan Mata a Wata Ƙaramar

A wani labari na daban, karamar hukumar Rano a Jihar Kano, a ranar Laraba ta amince da kafa dokar hana tadi ko haduwa tsakanin samari da 'yan mata da dare a jihar, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gidaje 5 na hafsoshin soja 'yan bindiga suka balle a NDA Kaduna

Karamar hukumar ta ce an saka wannan dokar ne saboda samun yaduwar badala da ake aikatawa tsakanin samari da yan mata har ma da zaurawa a yankin.

A cewar rahoton na Premium Times, karamar hukumar ta ce daga yanzu masoya suna iya haduwa ne kawai da rana domin yin tadi.

A cewar jami'in watsa labarai na karamar hukumar, Habibu Faragai, shugaban karamar hukumar, Dahiru Muhammad, ya sanar da dokar ne yayin taron tsaro da masu sarautun gargajiya da mazauna garin suka hallarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel