Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur, ta bayyana dalili

Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur, ta bayyana dalili

  • Matsalar tsaro a jihar Zamfara ta yi tsamari kuma gwamnatin jihar na shirin daukar matakan kare al’ummarta
  • Wasu gungun 'yan bindiga a jihar Zamfara sun mamaye garuruwa da dama inda suke sace mutane don neman kudin fansa
  • Makarantu da sauran cibiyoyin ilimi suma sun fuskanci hare-hare daga miyagun waɗanda ba su nuna jin ƙai a yayin aikinsu

Zamfara - An rufe dukkan manyan kasuwannin jihar Zamfara sakamakon umarnin Gwamna Bello Matawalle.

Kamar yadda gidan talabijin na Channels TV ya ruwaito, gwamnan ya kuma bayar da umurnin rufe dukkan gidajen mai dake yankunan.

Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur, ta bayyana dalili
Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur Hoto: Governor Bello Matawalle
Asali: Facebook

Ya kuma ba da umarnin cewa kada a sayar da mai ko da a cikin jarkoki.

TVC News ta rahoto cewa Matawalle ya ce matakin ya zama dole idan aka yi la’akari da dawowar fashi da makami da garkuwa da mutane a jihar.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Mun taba yi wa mutum 76 jana’iza a lokaci guda, babu wanda ya ji labari inji Sultan

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma umarci jami'an tsaro da su harbi kowane babur da ke dauke da mutane sama da biyu idan suka ki tsayawa don a kama su.

Rashin tsaro: Mun taba yi wa mutum 76 jana’iza a lokaci guda, babu wanda ya ji labari inji Sultan

A wani labarin, mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, yace ba a bada cikakken labari a kan irin kashe-kashen da ake fama da shi a yau.

Daily Trust ta rahoto Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III yana cewa sha’anin rashin tsaro ya yi kamari, ya kuma yi alkawarin cigaba da fadin gaskiya.

Da yake jawabi a wajen taron majalisar addinai na kasa a birnin tarayya Abuja, Sultan ya bada labarin wata rana da aka birne mutum 76 a garin Sokoto.

Kara karanta wannan

Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng