An yi jana'izar Musulmai 25 da matasan Irigwe suka kashe a garin Jos yau Asabar

An yi jana'izar Musulmai 25 da matasan Irigwe suka kashe a garin Jos yau Asabar

  • An bizne mutum 25 da wasu matasan Irigwa suka budewa wuta a Jos
  • Matasan na hanyarsu ta zuwa Ikare ne bayan halartan taron Zikiri a Bauchi
  • Hukumar yan sanda ta damke mutum shida kawo yanzu

An yi jana'izar matasan da halarci taron Zikirin kasa a jihar Bauchi 25 da yan bindigan kabilar Irigwe suka hallaka a Gada-biyu, karamar hukumar Jos ta Arewa a Jihar Plateau.

An bizne mamatan ne a makabartar Dadinkowa da cikin jihar, rahoton Daily Nigerian.

Jami'in gwamnatin mai suna Danladi Atu wanda ya ziyarci asibitin da aka kai wadanda suka jikkata yace mutum 25 aka tabbatar yanzu sun mutu.

Hakazalika kungiyar Miyetti Allah MACBAN tace ta kirga gawawwaki 25. Wakilin Miyetti Allah, Malam Nura Abdullahi yace: "Mun yiwa gawawwaki 25 wanka kuma muna shirin biznesu."

Kara karanta wannan

Yan sanda sun tabbatar da kisan mutum 22 a Jos, ana zargin matasan Irigwe suka kai hari

An yi jana'izar Musulmai 25 da matasan Irigwe suka kashe a garin Jos yau Asabar
An yi jana'izar Musulmai 25 da matasan Irigwe suka kashe a garin Jos yau Asabar Hoto: :Ado Abubakar Musa
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan sanda sun ce ana zargin matasan Irigwe ne

Wasu yan bindiga da ake zargin matasan Irigwe ne sun kai wa Musulmai matafiya 90 hari a jihar Plateau ranar Asabar, akalla mutum 22 sun mutu, yan sanda suka tabbatar.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Ubah Ogaba, ya bayyana cewa wasu matasa Kirista yan garin Irigwe suka kaiwa Musulman farmaki.

A cewarsa:

"Misalin karfe 0928hrs, hukumar yan sandan jihar Pleatuea ta samu labarin cewa wasu mahara da ake zargin matasan Irigwe ne (yawancinsu Kirista) sun kai hari kan motocin Musulmai biyar dake hanyar dawowa da taron Zikirin kasa a Bauchi kuma suka nufi Ikare a jihar Ondo."
"Mutum ashirin da biyu aka kashe yayinda 14 suka jikkata."

Jami'in yan sandan ya kara da cewa mutum 21 sun tsallake rijiya da baya.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Hukumar Hisbah a jihar Kano ta samu na ta kotun mai zaman kanta

Asali: Legit.ng

Online view pixel